Saura Kiris a Fara Zanga Zanga, Gwamnan Yobe Ya Sa Labule da Shugabannin Hukumomin Tsaro

Saura Kiris a Fara Zanga Zanga, Gwamnan Yobe Ya Sa Labule da Shugabannin Hukumomin Tsaro

  • Yanzu haka kasa da awanni 24 ya rage 'yan Najeriya su fantsama titunan kasar nan domin gudanar da zanga-zanga
  • Gwamnatin jihar Yobe ta fara shirin tarbar 'yan zanga-zangar cikin lumana ta hanyar samar da tsaro a sassan jihar
  • Mai Mala Buni ya gana da shugabannin hukumomin tsaron Yobe domin fitar da dabarun samar da tsaro yayin zanga-zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe - A gobe Alhamis ake sa titunan kasar nan za su cika da masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

A na ta bangaren, gwamnatin jihar Yobe ta fara shirin tabbatar da an samar da tsaro da bin doka da oda a sassan jihar.

Kara karanta wannan

"Ka samar mana da motoci": Masu zanga zanga sun tura bukatunsu ga gwamna

Mai Mala Buni
Gwamnatin Mai Mala Buni ta fara daukar matakan tsaro a lokacin zanga-zanga Hoto: Mohammed Goje
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Gwamna Mai Mala Buni ya gana da jagororin hukumomin tsaro a jihar a kan batun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Gwamnati na daukar matakan rage yunwa

Gwamnatin jihar Yobe ta ce ta na daukar matakan da za su saukaka halin matsin rayuwa da ake ciki.

Mataimakin gwamnan jihar, Idi Barde Gubana ne ya bayyana haka a madadin gwamna Mai Mala Buni bayan tattaunawa da jami'an tsaro.

Ya kara da cewa jama'a su yi hakuri, domin ana daukar matakan rage radadin da su ke ciki.

Gwamnati ta nemi addu'a kan matsalolin kasa

Gwamnatin Mai Mala Buni ta jihar Yobe ta nemi jama'a su taya shugabanni da addu'ar kawo gyara a kan kalubalen da su ka addabi kasa.

Gwamnan jihar ya nemi addu'o'in tare da bukatar shugabannin kananan hukumomi su wayar da kan jama'a a kan illar zanga-zanga.

Kara karanta wannan

"Ku yi hakuri, ku karawa Bola Tinubu lokaci," Kakakin majalisa ya roki masu shirin zanga zanga

'Yan daba sun nemi hana ayi zanga-zanga

A baya mun ruwaito cewa wasu 'yan daba a jihar Legas sun gargadi masu shirin fita zanga-zanga da su kuka da kansu tare da zamansu a gida.

An jiyo 'yan daban ta cikin wani bidiyo su na cewa ba za su bari a maimaita asarar da aka tafka a lokacin zanga-zangar EndSARS ba saboda muninsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.