'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Tsaro da Manoma a Wani Kazamin Hari a Sokoto

'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Tsaro da Manoma a Wani Kazamin Hari a Sokoto

  • Ƴan bindiga sun yi wa jami'an tsaro na rundunar tsaron jihar Sokoto kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Gudu ta jihar
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka jami'an tsaron mutum biyar tare da wasu manoma mutum biyu a ƙauyen Karfen Sarki
  • Ƙaramar hukumar Gudu na daga cikin ƙananan hukumomin jihar masu fama da matsalar rashin tsaro da ayyukan ƴan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Karfen Sarki cikin ƙaramar hukumar Gudu ta jihar Sokoto inda suka hallaka mutum bakwai.

Ƴan bindigan sun hallaka jami'an rundunar tsaron jihar mutum biyar da wasu manoma mutum biyu.

'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro a Sokoto
'Yan bindiga sun hallaka mutum bakwai a Sokoto Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro

Shugaban ƙaramar hukumar, Honarabul Umar Maikano Balle, ya tabbatar da cewa ƴan bindigan sun hallaka jami'an tsaron da manoman ne a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun sake dasa bam, ya hallaka babban jami'in gwammnati a Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun yi musu kwanton ɓauna yayin da suke aikin sintiri bayan samun bayanai cewa ƴan bindigan sun kafa sansani a yankin.

"Jajircewar jami'an tsaron mu ya rage ƙarfin hare-haren da ƴan bindiga ke kawowa."
"Sai dai, ƴan bindiga sun shammace su inda suka hallaka mutum biyar daga cikinsu."

- Honarabul Maikano Balle

An yi jana'izar mutane bakwai da aka hallaka yayin harin kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Ƙaramar hukumar Gudu na daga cikin ƙananan hukumomin jihar Sokoto 13 masu fama da matsalar ƴan bindiga.

'Yan bindiga: ƴan sanda sun yi magana

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa'i wanda ya tabbatar da aukuwar harin amma ya ce ba ya da cikakkun bayanai dangane da lamarin.

"Eh mun samu labarin kai harin, yanzu haka ina jiran rahoto daga wajen DPO. Idan na samu cikakkun bayanan zan kira daga baya."

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a shingen bincike

- ASP Ahmad Rufa'i

Ƴan bindiga sun sace basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari tare da yin awon gaba da Sarkin Gobir na yankin Gatawa, Isa Bawa tare da dan cikinsa.

Maharan sun yiwa basaraken kwantan ɓauna ne a daidai yankin Kwanar Maharba a lokacin da yake hanyar komawa gidansa a Sabon Birni daga Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng