"Ba a Najeriya Kaɗai Ake Wahala Ba," Fitaccen Sarki Ya Aika Saƙo ga Masu Shirin Zanga Zanga
- Wani Sarkin yarbawa ya yi kira ga masu shirin yin zanga-zanga kan tsaɗar rayuwa su yi haƙuri su karawa gwamnatin Bola Tinubu lokaci
- Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya ce wahalhalu da tsadar rayuwar da mutane ke kuka a kai, al'amari ne da ya shafi duk duniya
- Basarken ya ce duk da haƙƙin ƴan Najeriya ne su yi zanga-zanga amma su kaucewa lalata kadarorin gwamnati domin kansu abin zai dawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya yi kira ga matasan da ke shirin fita zanga zanga a watan Augusta su ƙara ba gwamnati lokaci.
Fitaccen sarkin yarbawan ya roki matasa su karawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu lokaci domin ta farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan da ya durƙushe.
Channels tv ta tattaro cewa mai martaba sarkin ya bayyana matsalar tsadar rayuwa da yunwar da ake fama da su a Najeriya a matsayin wani lamari na duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Busa haka Basaraken ya bukaci ƴan Najeriya su bai wa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ƙarin lokaci domin gyara matsalar hauhawar farashi.
Ooni ya roƙi matasa su ba Tinubu lokaci
Da yake jawabi a shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, Oba Ogunwusi ya ce:
"Eh tabbas abin da suke nanatawa gaskiya ne, muna shan wahala a kasar nan amma ba a Najeriya kadai ba, al’amari ne na duniya,”
"Ya zama dole mu yi kira (ga masu zanga-zangar) saboda akwai bukatar su ba gwamnatin tarayya ƙarin lokaci kadan domin saita komai tunda abu ne da ya taɓa duniya."
Sarkin ya jaddada cewa mutane na da ƴancin yin zanga-zanga amma ya kamata su kaucewa lalata kadarorin gwamnati da kayayyakin al'umma a lokacin, rahoton Daily Trust.
Matasa sun shirya gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ke ƙaruwa kullum a jihohi 36 da Abuja a watan Agusta, 2024.
Gwamna ya gana da masu shirin zanga-zanga
A wani rahoton kuma Gwamna Ademola Adeleke ya ja kunnen masu shirin zanga-zanga su guji duk abin da zai kawo tashin hankali a jihar Osun.
Gwamnan ya bayyana cewa duk da ƴan Najeriya na da ƴancin yin zanga-zanga amma gwamnatinsa ba za ta lamunci a riguza zaman lafiya ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng