Gwamna Abba Ya Dauki Mataki Kan Sabon Mafi Karancin Albashi Kwana 2 da Sa Hannun Tinubu

Gwamna Abba Ya Dauki Mataki Kan Sabon Mafi Karancin Albashi Kwana 2 da Sa Hannun Tinubu

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da kwamiti kan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata
  • Gwamnan ya buƙaci 'yan kwamitin su samo hanyoyin da gwamnatin za ta aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ba tare da ɓata lokaci ba
  • Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Gwarzo, ne ya ƙaɗdamar da kwamitin a gidan gwamnati a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da kwamiti kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa.

Ƙaddamar da kwamitin na zuwa ne sa’o’i 48 kacal bayan da Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kara alawus din 'yan NYSC zuwa N77,000? An gano gaskiya

Gwamna ya kaddamar da kwamiti kan mafi karancin albashi
Gwamna Abba ya kaddamar da kwamiti kan sabon mafi karancin albashi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Gwarzo ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya ja hankalin kwamitin albashi

Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Shuaibu, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce Gwamna Abba ya jaddada nauyin da ke kan kwamitin na yin tsari mai kyau kan sabon mafi ƙarancin albashin.

Ya kuma jaddada alhakin da ke kansu na samar da shawarwari kan yadda gwamnatin jihar za ta aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ba tare da ɓata lokaci ba, rahoton jaridar New Telegraph ya tabbatar.

Gwamna Abba ya ba da tabbacin cewa aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin zai ƙara kawo ci gaba a jihar ta kowane ɓangarori, domin gwamnati na ba da fifiko kan jindaɗin ma'aikata.

Kara karanta wannan

Ana harin zanga zanga gwamnati ta amince da ba da aikin da zai lakume N81bn

An ba kwamitin wa'adin makonni uku domin kammala aikin da aka sanya su.

Su wanene ƴan kwamitin karin albashin?

Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin mai ba da shawara na musamman ga gwamna kan harkokin jiha, Usman Bala.

Sauran 'yan kwamitin sun haɗa da kwamishinan kuɗi, Ibrahim Fagge, kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Alhaji Musa Shanono da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Baba Halilu Dantiye.

Sauran su ne Baffa Gaya, Farfesa Aliyu Isa Aliyu, Salahudeen Habib Isa, Ibrahim I. Boyi, Ibrahim Muhammad Kabara, Mustapha Nuraddeen Muhammad, Abdulkadir Abdussalam, Umar Muhammad Jalo, Hassan Salisu Kofar Mata da Yahaya Umar.

Gwamna zai biya mafi ƙarancin albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi magana kan batun biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 duk wata.

Gwamna Ademola Adeleke a ranar Juma'a, 19 ga watan Julin 2024 ya yi alƙawarin cewa zai biya ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashin na N70,000.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu a dokar sabon mafi ƙarancin albashi, bayanai sun fito

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng