Sojoji Sun Hallaka Ƙasurgumin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Mutane a Arewacin Najeriya

Sojoji Sun Hallaka Ƙasurgumin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Mutane a Arewacin Najeriya

  • Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka hatsabibin ɗan bindiga da ake nema ruwa a jallo a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas
  • Dakarun sojin sun kuma ƙwato makamai da kayan aiki bayan musayar wuta da tawagar ƴan bindigar a iyakar Taraba da Benue
  • Wannan nasara na zuwa ne a lokacin da ƴan Najeriya ke shirin zanga zanga kan tsadar rayuwa a watan Agusta mai kamawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Dakarun rundunar Birged ta shida sun samu nasarar hallaka ƙasurgumin ɗan bindigar da ake nema ruwa a jallo a jihar Taraba.

Dakarun sojojin na sashe na uku a rundunar Operation Whirl Stroke sun kashe ɗan ta'addan da ya addabi mutane a garuruwan da ke iyakar jihohin Taraba da Benue.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun sake dasa bam, ya hallaka babban jami'in gwammnati a Borno

Sojojin Najeriya.
Sojoji sun yi nasarar kashe ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar Taraba Hoto: Nigerian Army
Asali: Getty Images

Odumegu: 'Dan bindiga ya sheka barzahu

Gawurtaccen ɗan ta'addan mai suna Odumegu ya gamu da ajalinsa ne a kauyen Gbeji-Afia, wanda ke iyaka tsakanin Taraba da karamar hukumar Ukum a Benue.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukaddashin daraktan sashen hulda da jama’a na rundunar birged ta shida, Kyaftin Olubodunde Oni ne ya bayyana hakan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya ce dakarun sojojin sun samu nasarar kwato bindigu da alburusai bayan sheƙe ɗan ta'addan, rahoton Channels tv.

Yadda sojoji suka kashe ɗan bindigan

"Sojojin sun yi arangama da ƴan bindigar a kan babura ɗauke da makamai lokacin da suka fita sintiri, nan take dakarun suka tare su suka yi musayar wuta.
"Yayin musayar wutar ne sojojin suka halaka ɗan ta'adda ɗaya, sauran kuma suka arce ɗauke da raunukan harbin bindiga.
"Abubuwan da aka kwato sun hada da bindiga kirar AK 47 guda daya da magazine, harsashi na musamman guda bakwai, wayoyin hannu guda biyu, da kuma layu iri-iri.”

Kara karanta wannan

Abubuwan sani dangane da zanga zangar da za a yi a Najeriya

Sojoji sun samu wannan nasara ne a lokacin da ƴan Najeeiya ke shirin fita zanga-zanga a faɗin kasar nan, daga cikin dalilan su har da batun rashin tsaro.

Ƴan bindiga sun sace sarkin Gobir

A wani rahoton kuma, yan bindiga sun yi garkuwa da sarkin Gobir da ɗansa yayin da suke hanyar komawa gida a ƙaramar hukumar Sabon Birni a Sokoto.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Ahmed Rufai ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ƴan sanda sun fara bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262