Ana Shirin Zanga Zanga, Kashim Shettima ya Fadi Abin da Tinubu ke Bukata Daga 'Yan Kasa

Ana Shirin Zanga Zanga, Kashim Shettima ya Fadi Abin da Tinubu ke Bukata Daga 'Yan Kasa

  • Yayin da ya rage kwana daya tal 'yan Najeriya su fara zanga-zangar lumana ta kwanaki 10, gwamnati ta mika bukata ga 'yan kasa
  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na bukatar goyon bayan al'ummarsa
  • Kashim Shettima ya ce ta hanyar goyon bayan 'yan Najeriya ne shugaba Tinubu zai samu nasara wajen ci gaban da yake nufin kawowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya roki 'yan kasar nan su marawa shugaban Bola Ahmed Tinubu baya.

Sanata Kashim Shettima ya ce Mai girma shugaban kasar ya na da kyawawan manufofi da za su kawo ci gaban 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ku yi hakuri, ku karawa Bola Tinubu lokaci," Kakakin majalisa ya roki masu shirin zanga zanga

OfficialSKSM
Kashim Shettima ya bukaci a marawa shugaba Tinubu baya Hoto: @OfficialSKSM
Asali: Twitter

Bola Tinubu bai kaunar Musulmai da Arewa?

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin wakilan 'yan jarida daga Arewacin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce labarin da ake yadawa kan cewa shugaba Tinubu ba ya kaunar 'yan Arewa da musulmi ba gaskiya ba ne, domin za a gane hakan ta mukaman da ya nada.

"Akwai illoli tattare da zanga-zanga," Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce duk da 'yancin 'yan kasa ne gudanar da zanga-zanga, amma akwai babbar illa a hakan.

Ya ce wasu daga cikin abubuwan da zanga-zangar za ta iya haifarwa ba zai yi wa kowa dadi ba, kamar yadda Jaridar Leadership ta wallafa.

"Yau idan ka ce za a yi zanga-zanga, za ta haifar da asara. Zanga-zanga 'yancin yan kasa ne, amma bisa tarihi ana samun bata gari da ke shiga cikin lamarin."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya fadi abin da zai hana Tinubu shawo kan 'yan zanga zanga

- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasar ya ce Bola Tinubu na da manufofin ciyar da Arewacin Najeriya gaba.

Shettima ya amince ana wahala a mulkin Tinubu

A baya mun ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya amince 'yan Najeriya su na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa.

Amma Sanata Shettima na ganin tsunduma zanga-zangar gama gari ba za ta zama mafita daga cikin halin da ake ciki ba, domin yanzu lokacin magance matsalolin ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.