'Yan Sanda Sun Cafke Hadimin Sanata Ali Ndume, Sun Fadi Dalili
- Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Borno sun cafke hadimin Sanata Ali Ndume da wasu magoya bayansa mutum biyu a garin Biu da ke jihar
- Ƴan sandan sun kuma tafi da mutane zuwa birnin Maiduguri, babban birnin jihar inda suka ci gaba da tsare su a can
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da cafke su inda ya ƙara da cewa an yi kamun ne bayan samun bayanan sirri kan wani shiri da suke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Ƴan sanda a jihar Borno sun cafke hadimin Sanata Ali Ndume tare da magoya bayansa mutum biyu.
Ƴan sandan sun cafke mutanen ne a garin Biu sannan suka tsare su a Maiduguri, babban birnin jihar.
An buƙaci ƴan sanda su tausaya
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa matar hadimin ta tabbatar da cewa mijinta Shehu Usman Aliyu (Babandi), an cafke shi ne tare da wasu mutum biyu, Tasiu Hassan Malgwi da Ibrahim Adamu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina roƙon ƴan sanda da su saki mijina. Shi ne wanda muka dogara da shi, kuma muna ta shan wuya tun ranar da aka cafke shi."
- Matar hadimin Sanata Ali Ndume
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Lokacin da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya tabbatar da cafke mutanen.
ASP Nahum Kenneth Daso ya ƙara da cewa an cafke su ne saboda samun wani rahoton sirri kan shirinsu na gudanar da gangamin nuna goyon baya ga tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawan.
"An cafke su ne saboda wasu bayanan sirri kuma ana ci gaba da gudanar da bincike. Mun samu umarnin kotu dangane da tsare su da aka yi fiye da sa'o'i 24."
- ASP Nahum Kenneth Daso
Sauran magoya bayan Ali Ndume, sun ce an yi kamun ne saboda wani gangami da suka fasa wanda suka shirya saboda cire sanatan daga muƙaminsa a majalisa.
A makon da ya gabata dai wasu magoya bayan Ali Ndume sun yi shirin gudanar da gangami a Biu ranar Asabar, amma daga baya sun fasa bisa abin da suka kira rashin tsaron da ake fama da shi a jihar.
Karanta wasu labaran Ali Ndume da Majalisa
- Sanata Ndume ya yi magana kan zanga zangar matasa, ya kawo mafita 1
- Sanata Ali Ndume ya bayyana gwamna 1 a arewa da zainsa ya ci gaba da zama a APC
- Ana tunkarar zanga zanga, sanata Ndume ya ja da matakin majalisar dattawa
Ndume ya yi fatali da sabon muƙaminsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ali Ndume, ya yi watsi da naɗin da aka yi masa a matsayin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yawon buɗe ido.
Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya ba Sanata Ali Ndume sabon muƙamin biyo bayan tsige shi daga muƙamin mai tsawatarwa na majalisar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng