"Ku Yi Hakuri, Ku Karawa Bola Tinubu Lokaci," Kakakin Majalisa Ya Roki Masu Shirin Zanga Zanga

"Ku Yi Hakuri, Ku Karawa Bola Tinubu Lokaci," Kakakin Majalisa Ya Roki Masu Shirin Zanga Zanga

  • Majalisar wakilan kasar nan ta roki 'yan Najeriya su yi hakuri, kar su shiga zanga-zangar lumana ta kwanaki 10
  • Kakakin majalisar, Abbas Tajuddeen ne ya yi rokon a ranar Talata kwanaki biyu gabanin fara zanga-zanga da za a fara 1 Agusta
  • Rt. Hon. Abbas Tajuddeen ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta na bakin kokarinta wajen magance matsalar da ake fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kakakin majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya roki ƴan Najeriya su kara hakuri tare da ba wa gwamnatin tarayya lokaci ta gyara kasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta shata layi, ta hana masu zanga zanga zuwa wasu wurare idan an fito titi

Kakakin majalisar ya yi rokon ne a ranar Talata, inda ya shawarci 'yan Najeriya su hakura da batun tsunduma zanga-zanga a ranar Alhamis.

House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Majalisa ta nemi 'yan Najeriya su yi hakuri su fasa zanga-zanga Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba ya kasa a gwiwa wajen kokarin magance matsalolin da su ka addabi kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Majalisa na tattaunawa da matasa

Kakakin majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya ce majalisa ta na kokarin ganin an samu mafita a kan matsalar matsin rayuwa da ake fama da shi.

Channels Television ta wallafa cewa Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya kara da cewa su na kokarin tattaunawa da da matasa domin gano matsalolinsu.

"Gwamnati ta fara bijiro da hanyoyi da dama domin magance bukatu da muradun matasan kasar nan."
"Daya daga cikin hanyoyin nan ita ce bijiro da bayar da lamunin karatu domin rage nauyin da ke kan dalibai tare da tabbatar da cewa babu wanda aka tauyewa damar samun ilimi saboda kudi."

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

- Rt. Hon. Tajuddeen Abbas

Majalisa ta roki yan Arewa kan zanga-zanga

A wani labarin kun ji cewa yan majalisar tarayya daga Arewa maso Yamma sun nemi jama'ar da su ke wakilta su yi watsi da batun zanga-zanga saboda illarsa.

Jagoran 'yan majalisar, Sada Soli ya ce yankin Arewa maso Yamma sun sha wahala matuka, kuma ana fama da matsalolin tsaro da ta'addanci, saboda haka su guji zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.