Tsaftar Muhalli: Abba Kabir Ya Dauki Hanyar Gyara Bayan Maganar Hadimin Buhari

Tsaftar Muhalli: Abba Kabir Ya Dauki Hanyar Gyara Bayan Maganar Hadimin Buhari

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin kawo gyara kan tsaftar muhalli a fadin jihar domin kaucewa ambaliya
  • Abba Kabir Yusuf ya fara bayar da umurnin raba kayan aiki domin tsaftar muhalli a dukkan kananan hukumomin Kano
  • A makon da ya wuce ne hadimin shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga gwamnatin Kano kan yin ayyuka da suka shafi muhalli

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta dauki matakin tsaftar muhalli domin kare jihar daga ambaliyar ruwa a damunar bana.

Hakan na zuwa ne bayan hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi kira ga gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri: Ministan Tinubu ya ba 'yan Arewa shawari kan zanga-zangar da ake shirin yi

Gwamna Abba
Abba ya kaddamar da aikin tsaftar muhalli a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Abba Kabir Yusuf ya yi kan tsaftace magudanar ruwa ne a cikin sakon da daraktan yada labarn Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar da Bashir Ahmad ya yi wa Abba

A makon da ya wuce ne hadimin shugaba Buhari ya yi kira ga gwamnatin Kano kan yin ayyukan da suka shafi talakawa.

Legit ta ruwaito cewa Bashir Ahmad ya yi kira ga gwamnatin kan samar da ruwa, tsaftace muhalli da gyaran tituna a cikin birnin Kano.

Abba Kabir da tsaftar muhalli a jihar Kano

Gwamnatin NNPP mai-ci ta raba kayan tsaftace muhalli ga jami'an sa-kai 160 domin tsaftace magudanar ruwa a jihar Kano.

Ana sa ran cewa aikin tsaftar muhallin zai jawo kiyaye Kano daga ambaliyar ruwa da kawo ingantuwar lafiyar al'umma a jihar.

Kara karanta wannan

Harkar noma: Gwamnatin Kano ta ware biliyoyi domin aikin madatsar ruwa

A baya an yi ta korafin cewa babu kyawawan magudanar ruwa yayin da aka shigo damina.

Kayan da gwamnatin Kano ta raba

Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin tsafta da suka hada da cebur, baro, manjagara, safar hannu diga da dai sauransu.

Abba Kabir Yusuf ya yi kira na musamman ga al'ummar jihar su bayar da hadin kai wajen ganin an samu nasarar aikin.

Bashir Ahmad ya caccaki Abba Kabir

A wani rahoton a baya, kun ji cewa hadimin tsohon shugaban kasa Buhari, Bashir Ahmad, ya caccaki Abba Yusuf na Kano kan shirinsa na ganawa da Bola Tinubu kan tsadar rayuwa.

Gwamna Yusuf ya bayyana shirinsa na ganawa da shugaban kasar kan yiwuwar shiga tsakaninsa da yan kasuwa musamman saboda 'yan kasuwa a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng