Abubuwan Sani Dangane da Zanga Zangar da Za a Yi a Najeriya

Abubuwan Sani Dangane da Zanga Zangar da Za a Yi a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Matasa da dama sun shirya fitowa kan tituna domin gudanar da zanga-zanga kan halin ƙuncin da ake ciki a Najeriya.

Zanga-zangar dai an shirya ta ne domin nuna adawa da matsin tattalin arziƙi, tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayayyakin abinci da ƙaruwar talauci a ƙasa.

Ana shirin zanga-zanga a Najeriya
Matasa na shirin fitowa zanga-zanga a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

Abubuwan sani game da zanga-zanga

Ƴan siyasa da jami'an tsaro dai sun gargaɗi matasa kan fitowa domin zanga-zangar, amma masu shirya ta sun bayyana cewa dole sai sun fito domin gwamnati ta kai su maƙura.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ake shirin fara zanga-zangar a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, tashar Channels tv ta yi duba kan yadda abubuwa suke.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun canza shawara, sun faɗi matsaya kan zanga zangar da ake shirin yi

Wane hali tattalin arziƙin Najeriya ke ciki?

Najeriya na fama da matsalar tsadar rayuwa mafi muni a cikin shekaru biyo bayan sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

Tinubu ya cire tallafin man fetur da sakin Naira sakaka ta nemowa kanta daraja, wanda hakan ya sanya farashin man fetur ya ninka tare da hauhawar farashin kayayyaki.

Bankin duniya da asusun ba da Lamuni na duniya (IMF) sun ce ana buƙatar matakan ne domin farfado da tattalin arziƙin Najeriya yayin da gwamnati ta buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri.

Amma tsare-tsaren sun jefa ƴan Najeriya cikin wuya inda hauhawar farashin abinci ya kai kaso 40% cikin 100% sannan yunwa ta yaɗu musamman a Arewacin Najeriya.

Za a samu tashin hankali irin na Kenya? 

Wasu masu sharhi na ganin cewa zanga-zanga a Najeriya na iya ɗaukar salon da aka yi a Kenya, inda suka yi nuni da rawar da matasa masu yaɗa zanga-zangar a yanar gizo za su taka.

Kara karanta wannan

Ana sauran kwana 2, zanga zanga ta gamu da gagarumin koma baya a Arewa

Cibiyar SBM ta ce akwai yiwuwar zanga-zangar ta rikiɗe ta koma wani abu daban idan jami'an tsaro suka yi amfani da ƙarfin tuwo.

Sai dai, masana dama na ganin cewa zanga-zangar Najeriya ta bambanta da ta Kenya inda da wuya mutane da yawa za su fito duba da yadda aka murƙushe masu zanga-zanga a baya.

Su waye ke ɗaukar nauyin zanga-zangar?

Hukumomi sun ja kunnen matasan da ke son fitowa zanga-zanga waɗanda suka yi suna a shafukan sada zumunta ta hanyar yin amfani da taken "#EndBadGovernanceinNigeria"

Ƙungiyoyi da dama sun bayyana shirinsu na gudanar da zanga-zangar a cikin lumana.

Masu shirya zanga-zangar dai sun ce talakawan Najeriya ne ke jagorantar ta, inda suka zargi hukumomi da fara yunƙurin murƙushe zanga-zangar.

Me mutane suke cewa? 

Ana tsammanin cewa dai dubunnan ƴan Najeriya za su fito zanga-zangar a faɗin ƙasar nan, musamman a manyan birane irinsu Legas, Abuja da Kano.

Kara karanta wannan

"Shinkafa ta dawo N40,000" Gwamnatin Tinubu ta aika sako ga masu shirin zanga zanga

Mutane da dama sun nuna damuwa kan yiwuwar samun rikici ko rasa abin da suke samu a ranakun da za a gudanar da zanga-zangar.

Ya batun Arewa fa?

Matsin tattalin arziƙin da ake ciki ya yi tasiri sosai a Arewacin Najeriya, inda malaman addini ke ta kira ga matasa da su haƙura da fita zanga-zanga.

Sai dai, ƙungiyoyi da dama sun ƙudiri aniyar fitowa su nuna fushinsu kan halin da ake ciki a ƙasar nan.

Mutane da dama sun nuna za su yi biris da kiraye-kirayen da malamai ke yi na kada su fito zanga-zangar.

Me hukumomi suke cewa?

Mahukunta a Najeriya musamman gwamnoni da jami'an tsaro sun buƙaci matasa da kada su fito zanga-zangar.

Jami'an tsaro sun cafke wasu daga cikin matasan da suka fito suka yi kiran da a fito zanga-zangar.

Gwamnati ta amince da ƙara mafi ƙarancin albashi tare da ɗaukar matakan rage yunwa da suka haɗa da raba shinkafa a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Ana harin zanga zanga, gwamnatin tarayya ta dauki muhimmin mataki

Rundunar ƴan sanda a Abuja ta bayyana cewa za ta tura jami'ai 4,000 domin zanga-zangar.

Rundunar sojoji ta bayyana cewa ba za ta tsaya ta zura ido ba ta bari a samu karya doka da oda, rahoton RFI ya tabbatar.

Menene ya faru a baya?

Babbar zangar-zangar da aka yi a baya a Najeriya ta ƙare ne ta hanyar yin amfani da ƙarfin tuwo domin murƙushe masu zanga-zanga.

Zangar-zangar #EndSARS ta shekarar 2020 ta fara ne kan cin zalin da ƴan sanda na SARS suke yi, inda ta rikiɗe ta koma babbar zanga-zangar adawa da gwamnati a tarihin mulkin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Ƙungiyar Amnesty International ta ce sojoji sun hallaka aƙalla mutum 10 a Lekki da ke Legas. Gwamnati da rundunar sojoji sun musanta hakan.

A shekarar 2012, sojoji sun murƙushe zanga-zangar "Occupy Nigeria" wacce aka gudanar saboda niyyar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ta cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Babban malamin ƙasar Sudan ya aika muhhimmin saƙo ga matasan Najeriya

Matasa sun fice daga zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa atasa sama da miliyan ɗaya ƙarƙashin kungiyar matasan kiristocin Arewa sun tsame kansu daga zanga-zangar da ake shirin farawa ranar 1 ga watan Agusta, 2024.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban ƙungiyar matasan kiristocin Arewa, Rabaran Samson Job, ya fitar kan zanga-zangar da ake shirin yi a ƙasar nan

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng