Zanga Zanga: Gwamnatin Tinubu Ta Yanke Matsaya Kan Dawo da Tallafin Man Fetur

Zanga Zanga: Gwamnatin Tinubu Ta Yanke Matsaya Kan Dawo da Tallafin Man Fetur

  • Matasan Najeriya na shirin fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Agusta a dukkan jihohin ƙasar nan
  • Gwamnatin tarayya ta yanke matsaya kan maganar dawo da tallafin man fetur da matasan ke buƙata shugaba Bola Tinubu ya yi
  • Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Muhammad Idris ne ya yi bayanin a madadin Asiwaju Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi bayani kan abin da yasa ba za ta iya dawo da tallafin man fetur ba.

Bayanin na zuwa ne kasancewar matasa a fadin Najeriya na shirin fitowa kan tituna a dukkan jihohi domin yin zanga zanga.

Kara karanta wannan

An gaida matasa: Muhimman nasarori 3 da barazanar zanga zanga ta samar ga talakawa

Bola Tinubu
Gwamnati ya yanke hukunci kan talafin man fetur. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

DW Hausa ta wallafa bidiyon ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Muhammad Idris yana bayani kan dawo da tallafin man fetur a kafar Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta ce tallafin man fetur ya tafi

Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Muhammad Idris ya ce ba maganar dawo da tallafin man fetur a halin yanzu.

Muhammad Idris ya ce hakan ya zama dole kasancewar ba a sa tallafin man fetur a cikin kasafin kudin Najeriya ba.

Ministan ya kara da cewa a yanzu haka Najeriya ba ta da kudin da za ta biya kudin tallafin man fetur ko da tana son dawo da shi.

Matakin da gwamnatin Tinubu ta dauka

Ministan yada labaran ya ce a maimakon dawo da tallafi gwamnatin tarayya tana daukan matakin rage radadi ga yan kasa.

Matakan da gwamnatin take dauka sun hada da karin albashi, sauke farashin shinkafa da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Bankwana da tsadar fetur, gwamnati ta dauki mataki 1 na tallafawa matatar man Dangote

Saboda haka Muhammad Idris ya yi kira ga yan Najeriya su kara hakuri da zanga zanga domin nan gaba kadan za a samu yalwa a Najeriya.

Tinubu ya amince da karin albashi

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu a dokar sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000 a fadar shugaban ƙasa a Abuja.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke faɗi tashin kan yadda za ta daƙile zanga-zangar da matasa suka shirya yi a watan Agusta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng