Rundunar 'Yan Sanda Ta Sanya Dokar Ta Baci Domin Hana Zanga Zanga? Gaskiya Ta Fito

Rundunar 'Yan Sanda Ta Sanya Dokar Ta Baci Domin Hana Zanga Zanga? Gaskiya Ta Fito

  • Rundunar 'yan sanda ta yi martani ga wani rahoto da ake yadawa na cewa rundunar ta sanya dokar ta baci a ranakun zanga-zanga
  • A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar na kasa, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, rundunar ta ce wannan rahoton karya ne
  • ACP Adejobi ya ce babu wani umarnin dokar ta baci da sufeta janar na rundunar, Kayode Egbetokun ya bayar na hana zanga-zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa, sufeta janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun bai sanya dokar ta baci ba a kan zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.

Rundunar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da kakakinta kuma mataimakin kwamishina, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya rabawa manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnati da jami'an tsaro sun shiga matsala, lauya na neman diyyar N1bn

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan sanya dokar ta baci ga masu zanga-zanga
Rundunar 'yan sanda ta karyata rahoton sanya dokar ta baci a lokutan zanga-zanga. Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

'Yan sanda sun sanya dokar ta baci?

ACP Adejobi ya ce rahoton da ake yadawa bai fito daga rundunar ba kuma karya ne tsagwaronta, kamar yadda sanarwar da aka wallafa a shafin rundunar na X ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Wannan labarin na karya wani ra'ayi ne kawai na mawallafin wanda kuma ba ya wakiltar matsayar rundunar 'yan sandan Najeriya.
"Muna kira ga 'yan kasa da su yi watsi da wannan rahoto na cewar IGP ya sanya dokar ta baci, sannan su rika karbar irin wannan rahoton daga rundunar kai tsaye ko hukumar gwamnati."

Ta ina labarin sanya dokar ya fito?

Sanarwar da ACP Adejobi ya fitar ta ce wata kafar watsa labarai ce https://www.dockaysworld.com.ng/ wadda ta wallafa cewa sufeta janar na 'yan sanda ya kakaba dokar-ta-bacin.

Sanarwar ta ce rahoton karyar ya nuna cewa shugaban 'yan sandan ya ce dole ne masu zanga-zanga su dakatar da ita da zarar karfe 4:00 na yamma ya yi a kullum.

Kara karanta wannan

Adawa da gwamnatin Tinubu: Akpabio ya fallasa wadanda suka dauki nauyin zanga zanga

"Rundunar 'yan sanda na sanar da jama'a cewa sufeta janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun bai bayar da umarnin sanya wannan dokar ta bacin ba."

- Inji sanarwar.

Zanga-zanga: 'Yan sanda sun kama matashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sanda ta kama wani matashi da ya fito shafin Facebook yana kiran jama'a da su fito zanga-zanga tare da mamaye tituna.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da cafke matashin inda ya ce ana zargin kalaman matashin na iya tunzura jama'a su saba doka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.