Gwamna Ya Gana da Masu Shirin Yin Zanga Zanga, Ya Shata Layin da Ba Ya So a Ƙetare
- Gwamna Ademola Adeleke ya ja kunnen masu shirin zanga-zanga su guji duk abin da zai kawo tashin hankali a jihar Osun
- Gwamnan ya bayyana cewa duk da ƴan Najeriya na da ƴancin yin zanga-zanga amma gwamnatinsa ba za ta lamunci a riguza zaman lafiya ba
- Adeleke ya yi wannan gargaɗi ne yayin ganawa da masu shirya zanga-zangar da za a yi a gidan gwamnatinsa da ke Osogbo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya buƙaci masu shirya zanga-zangar da za a fara ranar 1 ga Agusta su yi ta cikin kwanciyar hankali da lumana.
Gwamnan ya gargaɗi masu ruwa da tsaki a zanga-zangar da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da zai tada zaune tsaye ba a lokacin.
Adeleke ya yi wannan kashedi ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Osun, Kolapo Alimi ya fitar ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adekele ya gana da masu shirin zanga-zanga
Sanarwar ta ce gwamnan ya yi gargaɗin ne a lokacin wani taro da masu shirya zanga-zangar da kungiyoyin fararen hula da jami’an tsaro a gidan gwamnatinsa.
Adeleke wanda mataimakinsa, Kola Adewusi ya wakilta a wurin taron ya ce zanga-zangar hakki ne na ƴan Najeriya wanda ba ba zai yiwu a tauye masu ba.
Amma ya jaddada cewa ba zai yi wu a fake da ita ba wajen ruguza zaman lafiya da kwanciyar hankalin jihar ba, cewar rahoton Punch.
Zanga-zanga: Gwamnan jihar Osun ya shata layi
A cewar Gwamna Adeleke, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Osun shi ya fi kamata ya zama abu mafi muhimmanci yayin gudanar da zanga-zangar.
“Don haka ina rokonku da ku kasance masu bin doka da oda kafin, lokacin da kuma bayan zanga-zangar da za a yi a fadin ƙasar nan, domin ba za mu lamunci tashin hankali ba," in ji shi.
Kungiyoyi sun janye shiga zanga-zanga
A wani labarin, an ji Matasan Najeriya sun kara gamuwa da cikas a shirinsu na fara zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati da suka jawo tsadar rayuwa.
Kungiyoyi da dama a Arewacin Najeriya sun sanar da janyewa daga zanga-zangar ranar Litinin saboda abin da suka alaƙanta da barazanar tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng