NIN: MTN Ya Rufe Ofisoshinsa a Fadin Najeriya, Ana Fargabar Jama’a Za Su Kai Farmaki

NIN: MTN Ya Rufe Ofisoshinsa a Fadin Najeriya, Ana Fargabar Jama’a Za Su Kai Farmaki

  • Kamfanin MTN ya yanke shawarar rufe dukkanin ofisoshinsa da ke a fadin Najeriya daga yau Talata, 30 ga watan Yulin 2024
  • MTN bai bayyana dalilin rufe ofisoshinsa ba amma ana kyautata zaton ba ya rasa nasaba da fargabar farmaki daga jama'a ba
  • Ko a jiya Litinin, an ga wasu fusatattun mutane suna lalata katangar ofishin MTN a wasu sassan kasar saboda rufe layin wayarsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa katafaren kamfanin sadarwa na MTN, ya rufe dukkanin ofisoshi da cibiyoyinsa a fadin Najeriya.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu masu hulda da MTN a fadin kasar suka fusata bayan da kamfanin sadarwar ya rufe layinsu a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Bankwana da tsadar fetur, gwamnati ta dauki mataki 1 na tallafawa matatar man Dangote

MTN ya aika sako ga abokan huldarsa bayan rufe layin wayoyinsu
MTN ya rufe ofisoshinsa na fadin Najeriya bayan farmakin jama'a. Hoto: @SirDavidBent (X)
Asali: Twitter

Mutane sun yi wa ofishin MTN tsinke

A wani faifan bidiyo da aka yada shi a kafafen sada zumunta a ranar Litinin, an ga wasu gungun mutane suna lalata katangar da ke wajen ofishin MTN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon, Nelson Akange ya ce fusatattun mutanen sun lalata katangar da ke ofishin MTN na unguwar Festac da ke jihar Legas saboda an rufe layin wayarsu.

Rahotanni daga wasu jihohin kasar sun nuna yadda mutane suka yi wa ofisoshin MTN tsinke a wani yunkuri na ganin an bude layin wayarsu da aka rufe.

MTN: 'Yan sanda sun magantu kan barnar

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya yi martanin kan faifan bidiyon da aka yada a shafin X, inji The Punch.

Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa DPO na FESTAC da mutanensa sun samu nasarar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wurin.

Kara karanta wannan

Hukumar NCC ta yi magana kan layukan da aka rufe, ta ba MTN, Airtel da sauransu umarni

"Wannan ba zai taba zama hanyar neman mafita ba."

- Inji Benjamin.

Kamfanin MTN zai rufe ofisoshinsa na Najeriya

Da yake mayar da martani a ranar Talata, kamfanin MTN ya ce zai rufe dukkanin ofisoshinsa na fadin kasar a yau.

"Abokan huldarmu, muna masu sanar da ku cewa za mu rufe ofisoshinmu da ke a faɗin ƙasar a yau, 30 ga Yuli, 2024."

Kamfanin ya fitar da wannan sanarwar ne a shafinsa na X a safiyar yau Talata, duba sanarwar a kasa:

Mutane sun aukawa ofishin MTN

Tun da fari, mun ruwaito cewa daruruwan masu amfani da layin MTN ne da cibiyar sadarwar ta rufe masu layukansu sun yi wa ofishin kamfanin da ke Ibadan.

An ce mutane sun yi wa ofishin tsinke ne bayan da kamfanin ya rufe layin wayarsu a ranar Lahadi bisa ikirarin cewa ba su yiwa layin rijista da NIN ba.

Kara karanta wannan

MTN sun rufe maka layi? Ga wata hanya mai sauki ta bude layukan da aka rufe

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.