Rashin Tsaro: Gwamnati ta Kai Daukin Tirelolin Abinci, Miliyoyin Kudi ga Mutanen Sokoto

Rashin Tsaro: Gwamnati ta Kai Daukin Tirelolin Abinci, Miliyoyin Kudi ga Mutanen Sokoto

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta kai gudunmawarsa tireloli hudu na abinci ga jama'ar da ta'addanci ya rutsa da su
  • Haka kuma an ware Naira Miliyan 10 ga mazauna karamar hukumar Isa domin rage masu halin rashin da su ke ciki
  • Gwamnatin ta kara samun tallafin Naira Miliyan 10 daga Sanata Aliyu Wamakko domin rabawa ga jama'ar yankin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta tallafawa mazauna ƙauyukan da ta'addanci 'yan bindiga ya rutsa da su da miliyoyin kudi da abinci.

Gwamnatin ta kai wa mazauna karamar hukumar Isa gudunmawar tirela hudu na abinci domin rage masu radadi.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri: Ministan Tinubu ya ba 'yan Arewa shawari kan zanga-zangar da ake shirin yi

Ahmed Aliyu Sokoto TV
Gwamnatin Sokoto ta raba tallafin kudi da abinci ga waɗanda 'yan ta'adda su ka addaba Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto TV
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa haka kuma gwamnatin ta ba yankin gudunmawar Naira Miliyan 10 domin rabawa ga mutanen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Sokoto ta fadi dalilin raba tallafi

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ce an raba tallafi kayan abinci da kudi ga wadanda ta'addanci ya shafa ne domin rage masu zafin da su ke ji.

Gwamna ya ce an raba tallafin ne ga iyalan wadanda 'yan bindiga su ka sace, ko su ka kashe a kwanakin nan a karamar hukumar Isa, Blueprint ta wallafa.

Sokoto: Gwamnati ta samu karin tallafin N10m

Gwamnatin jihar Sokoto ta samu tallafin Naira Miliyan 10 daga dan Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Aliyu Wamakko.

Gwamna Aliyu Ahmed ya bayyana takaicin halin rashin tsaro da jama'arsa ke ciki, tare da jaddada cewa su na daukar matakin daidaita lamarin.

Kara karanta wannan

Fargabar zanga zanga: Tinubu ya dawo biyan al'umma tallafi, an ci moriyar arzikin kasa

Ya ce an samar da hukumar tsaro domin inganta tsaro da kakkabe miyagu daga sassan jihar.

Gwamnati ta fara raba tallafin N50,000

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na fara raba tallafi ga 'yan Najeriya amma dauke da sharadi domin tallafawa Yan kasar nan.

Ministar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari, Doris Aniete ce ta bayyana fara rabon, lamarin da ya yi wa 'yan Najeriya dadi saboda halin da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.