“Ba Mu Bukatar Hakuri”: Malamin Musulunci Ya Soki Malamai Bayan Ganin Tinubu a Aso Rock

“Ba Mu Bukatar Hakuri”: Malamin Musulunci Ya Soki Malamai Bayan Ganin Tinubu a Aso Rock

  • Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya soki malaman Musulunci da suka gana da Shugaba Bola Tinubu kan halin kunci a kasa
  • Sheikh Dokoro ya ce bai kamata kawai malamai su gana da shi ba amma su zo su na ba al'umma hakuri da kuma tsare-tsare
  • Malamin ya ce ya kamata su fada masa abin da ya kamata domin tabbatar da aiwatar da abubuwa biyar masu muhimmanci a kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Malamin Musulunci a Gombe, Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya yi magana game da ziyarar malamai ga Bola Tinubu.

Malamin ya ce babu bukatar su zo da ba da hakuri ko kuma tsare-tsaren shugaban wadanda an riga an san su kuma sun wahalar da mutane.

Kara karanta wannan

"Rashin cin zabe ne": Ministan Tinubu ya tona asirin wadanda ke shirya zanga zanga

Sheikh Dokoro ya bukaci Tinubu ya aiwatar da abubuwa biyar a Najeriya
Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya bukaci Tinubu ya dawo da tallafin mai da na lantarki. Hoto: @Dolusegun (X), Sheikh Adamu Muhammad Dokoro.
Asali: UGC

Shehi ya soki malamai bayan ganin Tinubu

Sheikh Dokoro ya bayyana haka ne a wani karatunsa da ya wallafa bidiyo a shafinsa na Facebook a jiya Litinin 29 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun ji an ce wata tawaga ta ga shugaban kasa, kuma suna ta cewa mutane a yi hakuri, abin da kuka dauko kenan daga shugaban kasa a yi hakuri."
"Kawai kun je wurin shugaban kasa ya baku tsare-tsarensa, mu ne mu ke da kuka kawai a fada masa a cikin abubuwa biyar ya aiwatar da su."
"Ba mu bukatar tsare-tsarenka saboda sun wahalar da mu, ko ofis ba ka shiga ba ka cire tallafi domin haka ka dawo da shi."

- Sheikh Muhammad Adamu Dokoro

"Tinubu ka dawo da tallafi' - Sheikh Dokoro

Sheikh Dokoro ya kuma bukaci shugaban ya dawo da tallafin wutar lantarki da daga darajar Naira sannan samar da tsaro saboda manoma su je gona.

Kara karanta wannan

"Da Tinubu bai ci zaben 2023 ba," Minista ya fadi halin da Najeriya za ta shiga

Malamin ya ce za a iya ba shi zabi kan bude iyaka a shigo da abinci ko raba takin zamani ga manoman Najeriya.

Ya ce amma sauran guda hudu sun zama tilas a aiwatar da su saboda domin 'yan kasa ake mulki ba wai radin kan shugaban ba.

Sheikh Albaniy ya shawarci Tinubu

Kun ji cewa shehin malamin Musulunci a Gombe, Sheikh Adam Muhammad Albanin Gombe ya bukaci dawo da tallafin mai a Najeriya.

Malamin ya ce 'yan kasa ba su bukatar raba musu tirelolin shinkafa da aka shirya yi inda ya ce haka ba mafita ba ne a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.