Fargabar Zanga Zanga: Tinubu Ya Yi Wa Matasa Gata, Ana Sa Ran Su Fasa Hawa Tituna

Fargabar Zanga Zanga: Tinubu Ya Yi Wa Matasa Gata, Ana Sa Ran Su Fasa Hawa Tituna

  • Ana saura awanni kadan a fara zanga-zanga a Najeriya, Shugaba Bola Tinubu ya amince da kirkirar sakatariyar matasa
  • Tinubu ya dauki wannan matakin ne bayan korafin matasa a Abuja inda ya ke ganin hakan zai hana su shiga zanga-zanga.
  • Ministan Abuja, Nyesom Wike shi ne ya tura korafin matasan ga shugaban kasa inda nan take ya aiwatar da hakan gare su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da samar da sakatariyar matasa a birnin Abuja ana daf da zanga-zanga a kasar.

An amince da sakatariyar watanni kadan bayan samar da ta mata karkashin hukumar gudanarwa ta birnin Tarayyar Abuja, FCTA.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta ci sarautar gargajiya, wakili ya rasa rawaninsa saboda goyon bayan matasa

Tinubu ya amince da kirkirar sakatariyar matasa a Abuja
Yayin da ake shirin zanga-zanga, Bola Tinubu ya amince da kirkirar sakatariyar matasa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Tinubu ya amince da sakatariyar matasa

Wannan mataki na zuwa ne bayan bukatar Ministan Abuja ga shugaban domin cikawa matasan alkawari, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta tattaro cewa Wike ya yi alkawari ga matasan yayin wani taro a Abuja da matasan domin kashe musu guiwa wurin shiga zanga-zanga.

Ministan ya ce wannan sakatariya daidai take da ma'aikatar matasa a birnin wanda sakatare zai jagoranta kamar kwamishina.

"Ina da labarin mai dadi gare ku, bayan kun yi korafi, na kai kukanku zuwa ga shugaban kasa kuma ya amince da kirkirar sakatariyar matasa."
"Samar da tsaro shi ne babban abin da muka sanya a gaba yayin da aka amince da gina sabon ofishin 'yan sanda a kowace karamar hukuma a Abuja."

- Nyesom Wike

Wike ya yi alkawari ga matasan Abuja

Wike ya tabbatar da cewa ya tura korafinsu kan raba mukamai a Abuja bayan an nada wani daga jihar Kogi ya wakilci birnin.

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

Ya ce idan za a ba da mukamai a Abuja zai yi duba zuwa ga wurare na musamman a birnin domin su ma su samu wannan dama.

Diyar Tinubu ta yi magana kan zanga-zanga

Kun ji cewa 'yar shugaba Bola Bola Tinubu ta roki iyaye da su gargadi 'ya'yansu kan fita zanga-zanga musamman a jihar Lagos.

Folashade Tinubu ta koka kan yadda zanga-zanga ke jawo asarar dukiyoyi da kuma sace-sace musamman a baya da aka yi a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.