Ana Shirin Zanga Zanga, Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fitaccen Sarki a Arewa
- Ƴan bindiga sun yi garkuwa da sarkin Gobir da ɗansa yayin da suke hanyar komawa gida a ƙaramar hukumar Sabon Birni a Sokoto
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Ahmed Rufai ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ƴan sanda sun fara bincike
- Mazauna yankin sun tabbatar da cewa a ranar da aka sace sarkin Gobir, ƴan bindiga sun ɗauki wasu mutum biyar a garin Sabon Birni
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Ƴan bindiga sun kai hari tare da yin awon gaba da Sarkin Gobir na yankin Gatawa, Isa Bawa tare da dan cikinsa a titin Sakkwato zuwa Sabon Birni.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yiwa basaraken kwantan ɓauna a daidai yankin Kwanar Maharba a lokacin da yake hanyar komawa gida daga Sakkwato.
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin ga tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmed Rufai ya ƙara da cewa a halin yanzun dakarun ƴan sanda sun bazama, sun fara bincike da nufin kuɓutar da sarkin da ɗansa cikin ƙoshin lafiya.
Yadda 'yan bindiga suka sace Sarkin Gobir
Babban ɗan basaraken, Isa Gobir ya tabbatar da cewa ƴan bindiga sun tare mahaifinsa ne a hanyarsa ta dawowa gida a ƙaramar hukumar Sabon Birni.
Ya ce maharan sun buɗewa motar sarkin wuta wanda ya sa tayoyi suka fashe, direban ya yi cikin daji bisa tilas motar ta tsaya.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da hakimin da kuma ɗansa wanda ya tuƙo motar da suke ciki, rahoton Vanguard.
An bukaci a ceto Sarki da sauran mutane
Sakamakon haka Isah ya yi kira gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen kubutar da waɗanda harin ya rutsa da su.
Wasu majiyoyi a Sabon Birni sun ce lamarin ya haifar da tashin hankali da damuwa a tsakanin mazauna yankin, inda suka yi kira ga hukumomi su dauki mataki.
Sun ce ƴan bindigar sun sake yin garkuwa da wasu mutane biyar a yankin Sabon Birni a ranar da aka kai wa hakimin hari.
Bam ya halaka sojoji a jihar Borno
Kuna da labarin bam ya tashi da motar sojoji yayin da suke hanyar zuwa kauyen Kukawa da safiyar ranar Alhamis a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa duka sojoji bakwai da ke cikin motar sun mutu sakamakon fashewar bam ɗin a daidai kauyen Bawarti.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng