Adawa da Gwamnatin Tinubu: Akpabio Ya Fallasa Wadanda Suka Dauki Nauyin Zanga Zanga

Adawa da Gwamnatin Tinubu: Akpabio Ya Fallasa Wadanda Suka Dauki Nauyin Zanga Zanga

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana wadanda ke da hannu wajen daukar nauyin zanga-zangar tsadar rayuwa
  • Akpabio ya ce 'yan siyasar da suka gaza cimma manufarsu a lokacin babban zaben 2023 ne ke da hannu a zanga-zangar adawa da Tinubu
  • Ya ce wadanda suka shirya zanga-zangar suna tunanin shigowa mulki ta barauniyar hanya wanda hakan zai haifar da rikici a cikin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce ‘yan siyasar da suka fadi zabe a 2023 ne suka shirya zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin kasar.

Akpabio ya ce wadanda ake zargin sun dukufa wajen ganin sun samu mulki ko ta halin kaka, wanda hakan zai haifar da rikici a kasar.

Kara karanta wannan

'Yan siyasa da kungiyoyi da ke goyon bayan zanga zanga da wadanda suka kushe tsarin

Sanata Godswill Akpabio ya yi magana kan masu shirin yin zanga zanga
Sanata Godswill Akpabio ya gargadi masu shirin yin zanga-zanga. Hoto: @SPNigeria
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sabon mafi karancin albashi a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya zargi 'yan siyasa da zanga-zanga

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Akpabio ya yi kira ga matasan Najeriya da ka da su bari a yi amfani da su wajen lalata kasar.

Ya kuma yi nuni da kokarin da bangaren zartarwa da na majalisar dokoki ke yi na rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta a kasar nan.

“Mutanen da watakila ba su samu nasara a zaben 2023 ba ne ke tunanin za su iya hawa kan mulki ta bayan gida kuma hakan zai haifar da babban rikici.”

Akpabio ya gargadi masu zanga-zanga

A yayin zantawa da manema labarai, jaridar Tribune ta ruwaito shugaban majalisar dattawan na cewa:

Kara karanta wannan

"Gaskiyar abin da ya jawo ake shirin yin zanga-zanga", Farfesa Kperogi ya fasa ƙwai

"Ina cike da farin ciki. Ina matukar taya ma'aikacin Najeriya murna, domin wannan gyaran mafi karancin albashin da aka yi ya shafi kowa da kowa ne.
“Don haka, ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga masu yunkurin tada fitina cewa kuna da hakkin yin zanga-zanga. Amma ba ku da hurumin lalata kasar nan."

APC ta yiwa masu zanga-zanga martani

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugabannin jam'iyyar APC na jihohi 36 da birnin tarayya Abuja sun shirya gangami na mako biyu domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu.

A cewar kungiyar shugabannin jam'iyyar, za su yi wannan gangamin ne domin ya zama martani ga masu shirin yiwa gwamnatin Tinubu zamga-zanga kan tsadar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.