Kungiyar Duniya ta Goyi Bayan 'Yan Zanga Zanga a Najeriya, Ta Taso 'Yan Majalisa a Gaba
- Kwanaki biyu ya rage 'yan kasar nan su fita zanga-zangar lumana a birnin tarayya Abuja da sauran sassan Najeriya
- Kungiyar Action Aid ta bi sahun wasu kungiyoyi wajen kiran hukumomin tsaro da su kare rayuka da dukiyoyin jama'a a lokacin
- Kungiyar ta bayyana muhimmancin a kyale 'yan kasar nan su gudanar da zanga-zangar lumana cikin kwanciyar hankali
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Kungiyar da ke rajin kawar da talauci da kare hakkin dan Adam a Najeriya da wasu kasashe 45 na duniya ta Action Aid ta tunatar da hukumomin muhimmancin tsaro.
Action Aid na wannan batu ne a kan masu shirin gudanar da zanga-zangar lumana ta kwanaki 10 a kasar nan.
Jaridar Punch ta wallafa shugaban kungiyar na kasar nan, Andrew Mamedu na cewa duk dan kasa ya na da 'yancin bayyana bacin ransa ta hanyar zanga-zanga ba tare da tsoro ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zanga: An shawarci gwamnatin tarayya
Kungiyar Action Aid Nigeria ta shawarci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kar ayi amfani da karfi a kan masu zanga-zanga.
Ana sa ran za a gudanar da zanga-zangar lumana daga ranar Alhamis, 1 Agusta 2024 har zuwa 10 ga wata domin adawa da manufofin gwamnatin Tinubu.
An fadi matakin magance zanga-zanga
Shugaban kungiyar Action Aid na Najeriya, Andrew Mamedu ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnatin tarayya ta magance koken masu zanga-zanga.
Mista Mamedu ya bukaci 'yan majalisar tarayya su daina karbar alawus-alawus ba wai kawai rage albashi ba, Vanguard ta wallafa.
Idan aka rage kudin da ake biyan 'yan majalisar dattawa da wakilan tarayya, kungiyar ta na ganin za a iya magance wahalhalun talakawan Najeriya.
Matasa sun yi tattakin watsi da zanga-zanga
A wani rahoton kun ji yadda wasu matasa a jihar Legas su ka yi tattaki su na shawarartar jama'a su yi watsi da fita zanga-zanga a farkon watan Agusta.
Matasan da su ka taru a Lagos Island sun ce har yanzu ana jin illar zanga-zangar EndSARS, saboda haka bai kamata a maimaita irin wannan a bana ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng