'Yan Siyasa da Kungiyoyi da Ke Goyon Bayan Zanga Zanga da Wadanda Suka Kushe Tsarin

'Yan Siyasa da Kungiyoyi da Ke Goyon Bayan Zanga Zanga da Wadanda Suka Kushe Tsarin

A ranar 1 ga watan Agustan 2024 ne aka shirya fara zanga-zanga a fadin Najeriya kan halin kunci da ake ciki da tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Zanga-zangar ta samu goyon baya daga bangarorin kasar baki daya musamman daga matasa wadanda suke neman kawo sauyi a kasar.

'Yan siyasa da suka nuna goyon baya a yi zanga-zanga da kuma wadanda suka ki lamarin
An samu sabani tsakanin 'yan siyasa kan zanga-zanga a Najeriya. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

Duk da haka akwai wadanda suka nuna ba su tare da zanga-zangar inda suke ganin za a iya samun matsala saboda miyagu ka iya shiga ciki.

Legit Hausa ta jero muku 'yan siyasa da kungiyoyi da ke goyon baya ko kin amincewa da zanga-zangar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Matasa sun zama kishiyoyin 'yan zanga zanga, sun yi tattakin goyon bayan Tinubu

Wadanda ke goyon bayan zanga-zanga

1. Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya nuna goyon bayansa ga matasa masu zanga-zangar duba da halin da ake ciki.

Atiku ya bukaci matasan su gudanar da ita cikin lumana da tsarin doka inda ya shawarci gwamnati ta dauki matakin kawo karshen matsalolin.

2. Peter Obi

Shi ma dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya goyi bayan zanga-zangar inda ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da dama.

Obi ya ce ana ta zargin wasu na daukar nauyin zanga-zangar amma talauci da yunwa da sauran matsaloli su ne musabbabinta.

Sauran sun hada da:

  • Shugaban jam'iyyar SDP, Shehu Gabam
  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore
  • Kungiyar Amnesty International da sauransu.

Wadanda ba su goyon bayan zanga-zanga

1. Rabiu Kwankwaso

Sanata Rabiu Kwankwaso ya barranta da sauran 'yan takara inda ya bukaci matasa su sauya gwamnati ta hanyar akwatunan zabe.

Kara karanta wannan

Baraka ta shiga kungiyar yarbawa a kan zanga zangar adawa da manufofin Tinubu

Kwankwaso wanda ya yi takarar a jam'iyyar NNPP ya gargadi gwamnati da ta yi gaggawar kawo karshen matsalolin da ake ciki.

2. Malaman addinin Musulunci

Malaman Musulunci da dama sun haramta zanga-zanga inda suka ce kwata-kwata babu ita a tsarin addinin tare da gargaɗin matasa.

Matsayar malaman ta tada kura musamman a kafofin sadarwa inda wasu matasa ke zargin biyan malaman aka yi kan lamarin.

Sauran sun hada da:

  • Tsohon Ministan jiragen sama, Femi Fani-Kayode
  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri
  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo
  • Kungiyar sarakunan gargajiya ta Najeriya
  • Jama’atu Nasril Islam
  • Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN)

Diyar Tinubu ta yi magana kan zanga-zanga

Kun ji cewa 'yar Shugaba Bola Tinubu ta roki iyaye da su gargadi 'ya'yansu kan fita zanga-zanga musamman a jihar Lagos.

Folashade Tinubu ta koka kan yadda zanga-zanga ke jawo asarar dukiyoyi da kuma sace-sace musamman a baya da aka yi a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.