MTN Sun Rufe Maka Layi? Ga Wata Hanya Mai Sauki Ta Bude Layukan da Aka Rufe

MTN Sun Rufe Maka Layi? Ga Wata Hanya Mai Sauki Ta Bude Layukan da Aka Rufe

  • Hankula sun tashi daga ranar Lahadi zuwa yau Litinin bayan da kamfanin darwa na MTN ya rufe layukan daruruwan jama'a
  • Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin MTN ya rufe layukan mutanen da har yanzu ba su yiwa layukansu rijista da NIN ba
  • Bayan hayaniyar da kaure sakamakon wannan mataki, MTN ya fitar da matakai masu sauki na yadda za a bude layukan da aka rufe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - ‘Yan Najeriya da dama sun yi amfani da shafukan sada zumunta a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli, inda suka koka kan yadda aka rufe layukan su, musamman na MTN da Airtel.

Da yake martani, Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa a 2023 na jam'iyyar AAC, ya yi ikirarin cewa kamfanonin sadarwa sun rufe layukan ne saboda zanga-zangar da za a yi a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Yadda za a bude layin MTN da aka rufe saboda matsalar NIN cikin sauki

NIN: Matakai na bude layukan MTTN da aka rufe
Mataki mai sauki na bude layin MTN da aka rufe saboda matsalar NIN. MTN Nigeria, Ivan Pantic
Asali: Getty Images

Zanga-zanga ta sa aka rufe layin waya?

Omoyele Sowore ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a wani rubutu da ya wallafa a shafin X, Bashir Ahmad, tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karyata wannan ikirari na Sowore.

Bashir Ahmed ya ce wani babban jami'in gwamnatin tarayya ya tabbatar masa da cewa babu hannun gwamnati a rufe layukan da kamfanonin suka yi saboda hana zanga-zanga.

Businessday ta ruwaito cewa kamfanonin sadarwa sun fara rufe layukan waya da ba a yi masu rijista da NIN ba kwanaki kafin wa’adin NCC ya kare a ranar 31 ga Yuli, 2024.

Mataki mai sauƙi na bude layin MTN

  • A danna *996*NIN# a kan layin MTN da aka rufe saboda matsalar NIN.
  • Bayan awa 24 da danna *996*NIN#, sai a ziyarci shafin https://ninlinking.mtn.ng domin bude layin da aka rufe.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun mamaye ofishin MTN, an gano dalilin rufe layukan jama'a

Mai amfani da X din ya shawarci wadanda ba su haɗa layinsu da NIN ba su ziyarci shafin yanar gizon MTN domin ƙarin bayani kan yadda za su bude layinsu.

Jama'a sun mamaye ofishin MTN

A safiyar yau Litinin ne muka ruwaito cewa daruruwan masu amfani da layin MTN ne suka mamaye babban ofishin kamfanin da ke Ibadan, jihar Oyo.

An ce wasu daga cikin jama’ar da aka rufewa layinsu sun tayar da tarzoma a ofishin inda har suka rika jefa duwatsu a cikin ginin kamfanin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.