Litar Fetur Ta Koma N1,300 a Wajen Ƴan Bumburutu, NNPCL Ya Aika Sako Ga Ƴan Najeriya
- Rahotanni sun bayyana cewa babu mai a mafi yawan ma'ajiyoyin mai na kasar nan lamarin da ya jawo karancin mai a jihohin
- Sakamakon karancin man, ‘yan bumburutu sun fara cin karensu ba babbaka inda suke sayar da litar fetur kan N1,300 zuwa N1,500
- Kamfanin NNPCL dai ya shaidawa 'yan Najeriya cewa an samu karancin man ne sakamakon matsala da wasu jiragen ruwa suka samu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Da yawa daga cikin rumbunan ajiye man fetur a halin yanzu sun bushe, wanda hakan ya haifar da karancin man da kuma haddasa layukan ababen hawa a gidajen mai.
An ruwaito cewa wahalar fetur din a halin yanzu ta fi tsananta a jihohin Legas, Ogun, sassan Abuja, Neja, da wasu jihohin kasar nan, inda aka koma ga 'yan bumburutu.
Litar fetur ta koma N1,300-N1,500
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, ‘yan bumburutu sun fara cin karensu ba babbaka inda suke sayar da litar fetur kan N1,300 zuwa N1,500 a sassan jihohin Legas da Ogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dogayen layukan ababen hawa da aka fara yin su a gidajen mai a Abuja da Legas tun daga ranar Juma'a ya daga hankali inda abin ya kara kamari a farkon makon nan.
A yayin da muka ruwaito cewa gidajen man NNPC da ke sayar da da lita a kan N650, sauran gidajen man ‘yan kasuwa kuwa na sayar da kowace litar fetur tsakanin N850 zuwa N950.
Fetur: NNPCL ya aika sako ga 'yan kasa
Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa karancin man da ake samu ya samo asali ne daga matsalar da wasu jiragen ruwa guda biyu dauke da man suka samu.
NNPCL ya bayyana cewa:
“NNPC na son bayyana cewa tangardar samar da man fetur da rarraba shi da aka samu a wasu sassa kasar ya faru ne sanadin cikas da aka samu a ayyukan wasu jiragen ruwa guda biyu."
Kamfanin ya kara da cewa, "muna aiki ba dare ba rana tare da duk masu ruwa da tsaki donmin magance lamarin."
Sai dai duk da tabbacin da NNPC, lamarin ya kara ta’azzara yayin da rahotanni suka nuna cewa akwai dogayen layuka a gidajen mai da dama a biranen kasar, inji rahoton TV360.
NNPC zai nemo rancen $2bn
Sakamakon tabarbarewar lamura da kuma yadda kamfanin ke fuskantar matsala wajen shigowa da rarraba man fetur, kamfanin NNPCL zai karbo bashin dala biliyan biyu.
Mun ruwaito cewa shugaban kamfanin, Mele Kyari ya ce kudin za su taimakawa NNPCL wajen inganta ayyukansa musamman wajen wadatar da fetur a fadin kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng