Magana Ta Kare, Zanga Zangar Adawa da Tsadar Rayuwa Ta Barke a Kusa da Abuja

Magana Ta Kare, Zanga Zangar Adawa da Tsadar Rayuwa Ta Barke a Kusa da Abuja

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Neja na nuni da cewa matasa sun fara gudanar da zanga-zanga zangar adawa da tsadar rayuwa
  • Masu zanga zangar sun fito kan tituna ne dauke ta alluna suna rera wakokin da kira ga gwamnatin tarayya kan kawo saukin rayuwa
  • Zanga zangar na faruwa ne a jihar Neja kusa da Abuja duk da kokarin da gwamnan jihar ya yi na ganin ya shawo kan matasan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Matasa a jihar Neja sun barke da zanga zangar adawa da tsadar kayayyaki a Najeriya.

Rahotanni na nuni da cewa matasan sun fito ne a yankin Suleja da ke kusa da Abuja inda suke dauke da alluna da rubuce rubuce.

Kara karanta wannan

Minista ya fara ganawa da matasa, Nyesom Wike zai dakile zanga zanga a Abuja

Zanga zanga
Matasa sun fara zanga zangar tsadar rayuwa. Hoto: HurPhoto
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan jihar Neja ya yi kokarin shawo kan al'ummar jihar kan zanga zanga amma abin ya gagara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin hana zanga zanga a Neja

Rahotanni na nuni da cewa gwamna Muhammad Bago ya yi maganar raba tallafi ga yan jihar domin su hakura da zanga zangar.

Gwamna Bago ya yi alkawarin ba ma'ikata N20,000 da kuma sayar da abinci a farashi mai rahusa domin ganin ba su fita zanga zanga ba.

Neja: Matasa sun fito zanga zanga

A yau Litinin, 29 ga watan Yuli matasa suka fito tituna a yankin Suleja suna zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.

Premiuim Times ta ruwaito cewa matasan sun yi tattaki a kan titin Abuja-Kaduna inda suke rera wakokin nuna adawa da tsare-tsaren gwamantin tarayya.

Me matasan ke fada yayin zanga zangar?

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Peter Obi ya barranta da Kwankwaso, ya fadi masu daukar nauyinta

Rahotanni sun nuna cewa matasan na dauke da alluna da aka rubuta tsananin rayuwa ta yi yawa a Najeriya.

An ruwaito cewa wasu daga cikin matasan na ishara da cewa a dawo da tallafin man fetur da dai sauransu.

Zanga zanga: Dr Gumi ya canza matsaya

A wani rahoton, kun ji cewa babban malamin addinin Musulunci a Najeriya, Ahmad Mahmud Gumi ya canza matsaya kan fita zanga zanga da ake shirin yi.

Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana dalilan da suka sa ya canza matsayar duk da cewa ya goyi bayan fita zanga zanga a karon farko.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng