Kebbi: An Rasa Rai Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Jami'an Hukumar Kwastam

Kebbi: An Rasa Rai Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Jami'an Hukumar Kwastam

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan jami'an hukumar kwastam da ke aiki a jihar Kebbi wacce ke a yankin Arewacin Najeriya
  • Ƴan bindigan waɗanda suka kai harin a sansanin jami'an da ke garin Koko, sun hallaka jami'i ɗaya tare da yin awon gaba da wani jami'in
  • Kwanturolan hukumar na jihar ya sha alwashin cewa ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki a wani sansanin jami'an hukumar Kwastam a a garin Koko cikin jihar Kebbi.

Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka jami'in hukumar mutum ɗaya tare da yin awon gaba wani jami'in.

Kara karanta wannan

Dubun dan majalisa, hakimai masu hada baki da 'yan bindiga ta cika a jihar Arewa

'Yan bindiga sun farmaki jami'an kwastam a Kebbi
'Yan bindiga sun hallaka jami'in kwastam a Kebbi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar reshen jihar Kebbi, Muhammad Tajudeen Salisu, ya fitar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun biyo sahun jami'an ne har zuwa sansaninsu da ke Koko, sannan suka farmake su.

Kakakin ya ƙara da cewa sun lalata kayayyaki a sansanin tare da hallaka wani jami'i mai suna Dabo Umar.

Abin bai tsaya nan ba, an yi garkuwa da wani jami'i mai suna Babagana Abba Kabiru, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar da haka.

An tafi da gawar jami'in zuwa Kaduna domin yi masa jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Kwanturolan kwastam ya sha alwashi

Kwanturolan hukumar na jihar, Earnest Iheanacho, yayin da yake yi wa iyalan jami'in da aka kashe ta'aziyya, ya bayyana cewa an fara ƙoƙarin ceto jami'in da aka sace.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun zo da sabon ta'addanci, sun yi barna a ofishin 'ƴan sanda

"Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba ko tsoro ya sanya mu daina sintiri a kan iyakokinmu ba, muna nan kan bakanmu na murƙushe ayyukan fasa ƙwauri duk da barazanar da muke fuskanta daga wajen miyagu."

- Earnest Iheanacho

Ƴan bindiga sun hallaka ɗan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kashe wani Sufeton ƴan sanda mai suna Shehu Oyibo da wasu mutane uku a jihar Abia.

Ƴan bindigan sun kai harin ne lokacin da jami'an ƴan sandan ke tsaka da gudanar da aikin sintiri a ranar Lahadi, 21 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng