'Yan Kasuwa Sun Fadi Matsalar da Za a Samu Idan Dangote Ya Saki Man Fetur a Agusta

'Yan Kasuwa Sun Fadi Matsalar da Za a Samu Idan Dangote Ya Saki Man Fetur a Agusta

  • A yayin da aka samu sabani tsakanin Alhaji Aliko Dangote da gwamnatin tarayya kan matatarsa, wani lamari ya kara ɓullowa
  • Kungiyar yan kasuwa masu dillancin man fetur (IPMAN) ta bayyana babbar matsalar da za a fuskanta daga matatar man Dangote
  • Sai dai ƙungiyar IPMAN ta fadi hanya daya da kamfanin mai na NNPCL zai shigo cikin lamarin domin warware barazanar tsadar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Ba a gama warware rikicin tsakanin Aliko Dangote da gwamnatin tarayya kan matatarsa ba wata barazana ta ɓullo.

Kungiyar yan kasuwar man fetur ta kasa IPMAN ta ce ba za ta iya sayen mai daga matatar Dangote ba.

Kara karanta wannan

Muna tare da Dangote: 'Yan Najeriya sun kafe, sun ce dole gwamnati ta biyawa Dangote bukata

Matatar Dangote
IPMAN ta yi korafi kan matatar Dangote. Dangote Industries
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a watan Agusta ne matatar Dangote za ta fara samar da man fetur ga yan kasuwa a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IPMAN: 'Man Dangote zai yi mana tsada'

Kungiyar IPMAN ta bayyana cewa ba za ta iya sayen man fetur daga matatar Dangote ba saboda farashin zai kasance da tsada.

IPMAN ta ce farashin Dangote zai kasance ne irin farashin kasuwar duniya wanda ba zai haifar da riba ba a gidajen man Najeriya.

'Dangote bai yi mana magana ba' - IPMAN

Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN, Zarma Mustapha ya ce ba su samu bayani kan yadda farashin man Dangote zai kasance ba.

Zarma Mustapha ya bayyana cewa suna hasashen farashin man Dangote zai kasance da tsada saboda kudin da za a kashe kafin tace shi.

Menene mafita ga matatar Dangote?

Mataimakin shugaban IPMAN ya bayyana cewa mafita ita ce kamfanin NNPCL ya shigo cikin lamarin.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Bayan gargadin malaman Musulunci, Kungiyar CAN ta fadi matsayarta

Rahoton Television Nigeria ya nuna cewa Zarma Mustapha ya ce idan NNPCL ya saye man fetur a matatar Dangote sai ya rika sayar wa yan kasuwa a farashi mai sauki.

Kungiya ta yi kira ga Aliko Dangote

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Arewa Youth Assembly ta yi magana kan taƙaddamar da ake yi tsakanin Aliko Dangote da hukumomi.

Ƙungiyar matsan ta buƙaci Dangote da ya bi ƙa'idoji da dokokin hukumomin NMPDRA da NUPRC masu kula da ɓangaren mai a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng