Zanga Zanga: Sheikh Gumi Ya Canza Matsaya, Ya Ba Matasa Muhimmiyar Shawara
- Babban malamin addinin Musulunci a Najeriya, Ahmad Mahmud Gumi ya canza matsaya kan fita zanga zanga da ake shirin yi
- Dakta Ahmad Gumi ya bayyana dalilan da suka sa ya canza matsayar duk da cewa ya goyi bayan fita zanga zanga a karon farko
- Malamin ya bayyana abin da ya sa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasara a lokacin zanga zanga a 2012
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dakta Ahmad Mahmud Gumi ya yi sabon kira ga matasa kan zanga zanga.
Ahmad Gumi ya nuna fargaba kan rashin tsari da shugabanci cikin zanga zangar da matasan Najeriya ke shirin farawa a watan Agusta mai kamawa.
Legit ta tatttaro bayanan da Sheikh Ahmad Gumi ya yi ne a cikin wani bidiyo da Mahmud Muhammad Abu Farhaan ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Buhari suka samu nasarar zanga-zanga?
Dakta Ahmad Gumi ya bayyana cewa Muhammadu Buhari da wasu manyan APC sun samu nasara ne a lokacin zanga zangar 2012 ne domin suna da tsarin shugabanci.
Muhammadu Buhari da sauran manyan APC sun jagoranci zanga zanga a lokacin shugaba Goodluck Jonathan kan cire tallafin man fetur, kuma su ka cin ma nasara.
Zanga zanga: Gumi ya ba matasa shawara
Sheikh Gumi ya ce a wannan karon babu shugabanci da hadin kai a tafiyar zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.
Saboda haka ya ce ya kamata matasa su yi taka tsantsan domin idan ba shugabanci zanga zanga bala'i za ta haifar.
Gumi: Abin da ake fargaba a bana
Sheikh Gumi ya ce a 2012 babu fitinar yan Boko Haram, yan IPOB da masu garkuwa da mutane a Najeriya, lamarin da ya canza a zamanin yanzu.
Malamin ya ce a a halin yanzu yan ta'addar suna nan ta ko ina suna zuba ido wanda idan ba a kiyaye ba za su mayar da zanga zangar tarzoma.
Zanga zanga: Yan kasuwa sun dauki mataki
A wani rahoton, kun ji cewa fargabar afkuwar tashe-tashen hankula ya sanya yan kasuwa a jihar Kano taron gaggawa domin fitar da hanyoyin kariya.
Hukumar kasuwar ta kafa kwamitin tsaro dauke da mutane 20 domin kare shagunansu daga wadanda ka iya kai masu hari yayin zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng