Zanga Zanga: Peter Obi Ya Barranta da Kwankwaso, Ya Fadi Masu Daukar Nauyinta
- Dan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2023, Peter Obi ya fadi matsayarsa kan shriin zanga-zanga da matasa ke yi
- Obi ya bayyana cewa hakkinsu ne na 'yan kasa su gudanar da zanga-zanga kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su dama a Najeriya
- Jigon jam'iyyar LP ya ce ya kamata shugabanni su yi gaggawar kawo mafita a Najeriya duba da halin kunci da ake ciki a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Abia - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya yi magana kan shirin zanga-zanga a Najeriya.
Peter Obi ya goyi bayan zanga-zangar inda ya ce hakkin 'yan kasa ne gudanar da ita cikin lumana ba tare da rigima ba.
Zanga-zanga: Peter Obi ya fadi matsayarsa
Tsohon gwamnan Anambra ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da Channels TV ta wallafa a yau Lahadi 28 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi ya ce babu masu daukar nauyin zanga-zangar illa yunwa da da rashin tabbas kan makomar kasar da kuma talauci.
"Idan suna maganar masu daukar nauyin zanga-zanga, ce musu na ke ai amsar mai sauki ce, yunwa ne da rashin tabbas tsakanin matasa."
- Peter Obi
Obi ya shawarci jami'an tsaro kan zanga-zanga
Peter Obi ya ce hakan shi zai tabbatarwa da shugabanni cewa matasa suna dauke da korafi duba da halin da ake ciki a yanzu.
Tsohon dan takarar ya ce tabbas babu wanda ya isa a yanzu ya ce ba a cikin matsanancin halin kunci a kasar baki daya.
Ya bukaci jami'an tsaro da su ba masu zanga-zangar kariya domin gudanar da ita cikin lumana ba tare da matsala ba.
Kwanwkaso ya shawarci matasa masu zanga-zanga
Mun kawo muku labarin cewa Sanata Rabiu Kwanwkaso ya magantu kan shirin zanga-zanga da matasa ke yi a Najeriya.
Kwanwkaso karara ya nuna cewa zanga-zanga ba ita ba ce mafita inda ya tabbatar da cewa ana cikin wani hali a kasar.
Sanatan ya ce ya kamata mutane su yi amfani ne da akwatin zabe wurin kawar da azzaluman shugabanni da suka saka jama'a a kunci.
Asali: Legit.ng