Ana Maganar Yunwa, Sarakuna Sun Dami Tinubu Ya Samar da Sababbin Jihohi
- Gamayyar sarakunan gargajiya a Kudu maso Gabashin Najeriya sun roki Shugaba Bola Tinubu alfarma a yankin
- Sarakunan sun bukaci karin jihohi biyu a yankin da ke da guda biyar saboda daidaito da sauran yankunan kasar
- Wannan na zuwa ne yayin da wasu bangarorin kasar ke neman kirkirar sababbin jihohi ciki har da jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, sarakunan gargajiya a yankin Kudu maso Gabashin kasar sababbin jihohi ne a gabansu.
Sarakunan sun matsawa Shugaba Bola Tinubu da ya yi mai yiwuwa domin samar da sababbin jihohi guda biyu a yankin.
Sarakuna sun roki Tinubu alfarma a yankinsu
Masu sarautar sun bayyana haka ne a birnin Abuja inda suka ce karin jihohin zai taimaka wurin cigaban yankin, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban tawagar, Igwe Samuel Asadu ya ce bukatar tasu ga Tinubu sun cimma ta ne a ganawar kwamitin kungiyar na karshe.
Basarake Asadu ya ce samar da sababbin jihohin zai tabbatar da daidaito tsakaninsu da sauran yankunan Najeriya, Tribune ta tattaro.
Ya ce yankin Kudu maso Gabas ne kadai ke da jihohi biyar sabanin sauran wanda har da yanki mai jihohi bakwai.
"A ganawar da muka yi na masu sarautar gargajiya, mun ce za mu amince da kirkirar sabuwar jiha a yankin Kudu maso Gabas."
"Mun hada kanmu a wannan gwagwarmaya, muna da jihohi biyar a yankinmu, muna son samun karin biyu su zama bakwai."
"Amma duk abin da muka samu daga shugaban kasa muna godiya, muna neman taimakonsa ubangiji ya taimake shi kan wannan aiki."
- Igwe Samuel Asadu
Wannan bukatar tasu na zuwa ne yayin da Tinubu ke cikin matsi kan zanga-zanga da za a gudanar a kasar.
Kano: Sumaila ya mika kudirin jihar Tiga
A wani labarin, kun ji cewa Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya gabatar da kudirin kirkirar sabuwar jiha a Kano.
Sumaila ya mika kudirin ne domin kirkirar sabuwar jihar Tiga da za ta fito daga cikin Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Asali: Legit.ng