“Ba Lagos a Ciki”: Diyar Tinubu Ta Yi Magana Kan Zanga Zanga, Ta Shawarci Iyaye

“Ba Lagos a Ciki”: Diyar Tinubu Ta Yi Magana Kan Zanga Zanga, Ta Shawarci Iyaye

  • Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, diyar Shugaba Bola Tinubu ta yi magana kan shirin da matasa ke yi a kasar
  • Folashade Tinubu ta ce su a jihar Lagos ba za su fito zanga-zanga ba inda ta ba iyaye shawara game da gargadin 'ya'yansu
  • Folashade ta bayyana irin matsalolin da aka samu lokacin zanga-zangar EndSARS da aka yi inda ta ce an samu asarar dukiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - 'Yar Shugaba Bola Tinubu, Folashade Tinubu ta yi magana kan shirin zanga-zangar matasa a Najeriya.

Folashade ta tabbaatar da cewa babu wata zanga-zanga da za a yi a jihar Lagos a ranar 1 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Manyan Arewa sun hakura da shiga zanga zanga, sun ba matasa shawara

'Yar Tinubu ta gargadi masu shirin yin zanga-zanga
Diyar Bola Tinubu da ake kira Folashade Tinubu ta yi magana kan masu zanga-zanga. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Folashade Tinubu-Ojo.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Diyar Tinubu ta gargadi iyaye

'Yar shugaban ta bayyana haka yayin da take jawabi ga 'yan kasuwa inda ta ce akwai rashin adalci daga jama'a, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce gwamnatin da ba ta yi ko shekara uku ba bai kamata a caccake ta ba saboda tana bukatar lokaci a ga kamun ludayinta.

Har ila yau, ta bukaci iyaye da su gargadi 'ya'yansu daga fita zanga-zangar da za a fara a ranar 1 ga watan Agustan 2024, Punch ta tattaro.

Folashade ta ce babu zanga-zanga a Lagos

"Kafin kuce gwamnatin ba ta tsinana komai ba, ya kamata ku ba ta dama ta yi akalla shekaru uku a kan mulki."
"Mu fadawa 'ya'yanmu da 'yan uwanmu cewa babu zanga-zanga a Lagos, ku tuna wanda suka yi a baya yadda aka lalata mana dukiyoyi."
"Bai kamata ku bar 'ya'yanku wasu su yi amfani da su ba wurin ba su kudi domin su lalata dukiyoyin jama'a da fadace-fadace."

Kara karanta wannan

"Tinubu yana taya ku zanga zangar": Gwamnati ta lissafo shirin shugaban ga matasa

- Folashade Tinubu

Legit Hausa ta ji ta bakin wani a Lagos

Wani matashi a jihar Lagos, Ajayi Joseph ya fadawa Legit Hausa ra'ayinsa kan maganar Folashade Tinubu.

Ajayi ya ce Folashade ta fadi ra'ayinta ne amma maganarta ba zai yi tasiri a wurin matasa ba saboda halin da ake ciki.

Ya bukaci gwamnati ta yi gaggawar daukar mataki duk da yanzu za a iya cewa lokaci ya kure amma dai an tafka kuskure tun farko.

Wike ya roki al'umma karin hakuri

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana kan zanga-zanga da ake shirin fita a Najeriya.

Wike ya bukaci matasa da sauran 'yan kasa da su ba Bola Tinubu karin lokaci tare da uzuri domin kawo karshen matsalolin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.