Shirin Zanga Zanga a Kano: 'Yan Sanda sun Mika Bukatunsu ga Matasa
- Dukkanin masu ruwa da tsaki, musamman hukumomin tsaron Najeriya sun fara daura damarar tunkarar zanga-zanga da ake shirin yi
- Rundunar 'yan sanda a Kano ta gudanar da muhimmin taro da sauran shugabannin hukumomin tsaro a jihar domin hana ayyukan miyagu
- Daga cikin shugabannin da aka zauna da su akwai sojoji da hukumar tsaron fararen hula da bijilanti da hukumar hana fasa kwauri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa yayin da wasu matasa ke shirin shiga zanga-zanga, su ma sun shirya tunkarar lamarin a mako mai zuwa.
Jami'in hulda da rundunar na Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa sun zauna da sauran shugabannin hukumomin tsaro domin fitar da hanyar da za a tarbi zanga-zanga a jihar.
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, SP Kiyawa ya bayyana cewa sun fitar da matakai da dama da za su taimaka wajen gudanar da zanga-zanga a cikin lumana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu matakai aka dauka kan Zanga-zanga?
Rundunar yan sandan Kano ta ce za ta yi aiki da sauran jami'ai wajen dakile yunkurin masu shirin tayar da hankula a lokutan zanga zanga.
Radio Nigeria ta wallafa cewa yan sandan na cikin shirin kar-ta-kwana domin tabbatar da ba a salwantar da rayuka ba idan an fara zanga zanga.
Zanga-zanga: Yan sanda sun mika bukatunsu
Rundunar yan sanda ta mika jerin bukatunta ga masu shirin shiga zanga-zangar gama gari da za a fara daga 1-10 Agusta, 2024.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar ya lissafa bukatunsu da suka hada da ba su bayanan a kan hanyoyin da za a bi, lokacin da za a fara da kuma kammala da sunayen jagororin zanga-zangar.
Kwankwaso ya fadi mafita a madadin zanga-zanga
A baya kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayar da mafita da za ta fi alheri ga 'yan kasar nan a maimakon tsunduma zanga-zanga.
Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa kamata ya yi jama'a su tanadi katunan zabensu domin kawar da gwamnatin Bola Tinubu a kakar zabe mai zuwa tun da ta gaza tafiyar da kasar.
Asali: Legit.ng