“Rashin Cin Zabe Ne”: Ministan Tinubu Ya Tona Asirin Wadanda Ke Shirya Zanga Zanga

“Rashin Cin Zabe Ne”: Ministan Tinubu Ya Tona Asirin Wadanda Ke Shirya Zanga Zanga

  • Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana mai kama hankali ga matasa
  • Ministan ya roki al'ummar Najeriya da su kara hakuri yana da tabbacin Bola Tinubu yana kokarin kawo gyara kuma kwararre ne
  • Wike ya zargi wasu 'yan siyasa da ba su yi nasara a zabe ba da shirya wannan zanga-zanga domin kifar da gwamnatin Tinubu a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana damuwa kan masu shirin yin zanga-zanga musamman a Abuja.

Wike ya ce zai dakile duk wani shiri na zanga-zangar a birnin saboda mummunan manufa da ke cikin lamarin.

Kara karanta wannan

"Da Tinubu bai ci zaben 2023 ba," Minista ya fadi halin da Najeriya za ta shiga

Ministan Tinubu ya gano masu son kawo rigima a zanga-zanga
Nyesom Wike ya zargi wadanda suka fadi zabe da kitsa zanga-zanga. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nywsom Ezenwo Wike.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Wike ya zargi wasu 'yan siyasa

Ministan ya bayyana haka ne yayin wani babban taro a Abuja a jiya Asabar 27 ga watan Yulin 2024, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya ce wasu ne da ba su yi nasara a zabe ba suke son tada rigima domin samun damar kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Ya bukaci al'umma da su kara ba Tinubu lokaci inda ya ce yana da tabbacin shugaban zai kawo sauyi ba da jimawa ba, Punch ta tattaro.

Wike ya roki masu yin zanga-zanga

Har ila yau, ya roki masu shirya zanga-zangar da su janye kudirinsu inda ya ce hakan kawai zai kara kawo koma-baya ne ga kasar.

"Akwai wasu 'yan siyasa da ke son mulki ta kowace hanya, su ne wadanda suka rasa nasara a zabe."

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri: Ministan Tinubu ya ba 'yan Arewa shawari kan zanga-zangar da ake shirin yi

"Hanya daya domin samun dama a gare su ita ce kifar da gwamnati ta kowane hali, ba za mu bari ba."

- Nyesom Wike

Zanga- zanga: Wike ya roki al'umma karin hakuri

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana kan zanga-zanga da ake shirin fita a Najeriya.

Wike ya bukaci matasa da sauran 'yan kasa da su ba Bola Tinubu karin lokaci tare da uzuri domin kawo karshen matsalolin.

Wannan na zuwa ne yayin da matasa ke shirin yin zanga-zanga duba da halin kunci da ake ciki a fadin kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.