Zanga Zanga: 'Yan Kasuwa a Kano Sun Dauki Matakin Tsare Dukiyoyinsu
- Fargabar afkuwar tashe-tashen hankula ya sanya yan kasuwa a jihar Kano taron gaggawa domin fitar da hanyoyin kariya
- Hukumar kasuwar ta kafa kwamitin tsaro dauke da mutane 20 domin kare shagunansu daga wadanda ka iya kai masu hari yayin zanga-zanga
- 'Yan Najeriya sun fusata inda su ka shirya fita zanga-zangar kwanaki 10 domin tunatar da gwamnati ta waiwaye su domin nemo mafita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - A lokacin da ya rage kwanaki yan Najeriya su tsunduma zanga-zangar gama gari, yan kasuwa a Kano sun yi taron kare dukiyoyinsu.
A ranar Asabar ne kungiyar 'yan kasuwa ta kafa kwamitin mutane 20 da za su fitar da tsare-tsaren tabbatar da tsaro a kasuwanni.
Jaridar Punch ta wallafa cewa jagoran 'yan kasuwar Kano, Alhaji Sabiu Bako ya shaidawa manema labarai cewa sun gana da masu manya manyan kantina a jihar da sauran 'yan kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan kasuwa sun fadi dalilin matakan tsaro
A zantawarsa da manema labarai, shugaban yan kasuwar kantin kwari a Kano, Balarabe Tatari ya ce su na da masaniyar zanga-zangar lumana aka shirya.
Amma a cewar shugaban kasuwar, akwai fargabar bata gari za su iya kawo farmaki kasuwanni domin satar kaya, wanda ya sa aka dauki matakin riga-kafi, Solacebase ta wallafa.
" A irin wadannan lokutan ne bata-gari ke amfani da damar wajen kai hare hare, tare da satar kaya da lalata wasu."
- Shugaban kasuwar kantin kwari, Balarabe Tatari
An ba wa masu zanga-zanga shawara
Yan kasuwar Kano sun shawarci masu shirin fita zanga zanga da su gujewa tayar da hankula da sace-sace yayin tura sakonsu ga gwamnati.
Shugaban kasuwar kantin kwari, Balarabe Tatari ne ya bayar da shawarar a taron manema labarai ranar Asabar.
Yan sanda sun fadi illar zanga zanga
A baya mun ruwaito cewa rundunar yan sandan kasar nan ta ce zanga-zanga za ta iya jawo matsaloli da yawa, inda aka bayar da misali da kasashen ketare da har yanzu ke fama da irin matsalar.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, reshen jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya ce za a iya samun tashe-tashen hankula da zai jawo asarar rayuka da lalata dukiyoyin gwamnati.
Asali: Legit.ng