“Da Tinubu Bai Ci Zaben 2023 ba,” Minista Ya Fadi Halin da Najeriya Za Ta Shiga
- An yi kira ga matasa masu shirin yin zanga-zanga da su janye tare da ba gwamnati goyon baya wajen samar da ababen more rayuwa
- Ministan ayyuka, David Umahi ya yi wannan kiran a lokacin da yake kaddamar da wani shiri na Operation Free Our Roads” a Abuja
- Mista Umahi ya yi ikirarin cewa da yanzu Najeriya ta lalace idan da ubangiji bai sa Bola Tinubu ne shugaban kasa a yanzu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce da yanzu Najeriya ta karasa lalacewa idan da ubangiji bai ba Bola Tinubu nasara ba a zaben 2023.
Mista David Umahi ya ce kasancewar Bola Tinubu shi ne shugaban kasar Najeriya a wannan 'mawuyacin hali' ya sa kasar ba ta lalace ba.
Ministan ya fadi haka ne a lokacin da yake kira ga matasa da su hakura da zanga-zanga tare da tallafawa gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Da yanzu Najeriya ta lalace" - Umahi
Mista Umahi, wanda ya kaddamar da shirin gwamnatin tarayya mai taken “Operation Free Our Roads” a Abuja ya ce Tinubu zai kawo sauyi a kasar idan aka kara masa lokaci.
Ministan, ya ce an kaddamar da shirin ne da nufin ganin dukkanin hanyoyin da ake ginawa sun kasance wadanda za a iya amfani da su kuma an kammala su a kan lokaci.
A cewar Umahi:
“Bari in yi amfani da wannan damar in yi kira ga matasanmu da su kara ba Bola Tinubu lokaci. Da yanzu kasarmu ta lalace idan da ubangiji bai kawo Tinubu a irin wannan mawuyacin halin ba.
"Mutane da yawa ba su san irin kalubalen da muka fuskanta kafin Tinubu ya hau karagar mulkin kasar ba.”
Minista ya roki matasa kan zanga-zanga
Ministan ayyukan ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu kishin kasa tare da taimakawa gwamnati wajen sake dawo da martabar kasar nan.
Jaridar The Sun ta ruwaito cewa Mista Umahi ya ce zanga-zangar da ake shirin yi na iya zama hanyar da bata gari za su tayar da zaune tsaye.
“Kwarai ana iya fuskantar wahalhalu, amma dole ne safiya tayi bayan ketowar alfijir; mun ga yakini da jajurcewa a tare da Shugaba Bola Tinubu.
Don haka, mu kara ba shi lokaci, mu ba shi goyon baya, mu kara samar da ayyukan yi, kasarmu za ta sake zama abar alfaharinmu.”
- A cewar Umahi.
Kperogi: "Abin da ya jawo zanga-zanga"
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mai sharhi kan al'amuran siyasa da zamantakewar Najeriya, Farfesa Farooq Kperogi ya ce yunwa da rashin tabbas suka jawo zanga-zanga.
Farfesa Kperogi ya ce daga lokacin da 'yan Najeriya suka kai magaryar tukewa kan halin da suke ciki, to ba sa bukatar wani dan jagora wajen yin adawa da 'yan siyasar kasar.
Asali: Legit.ng