“Gaskiyar Abin da Ya Jawo Ake Shirin Yin Zanga-Zanga”, Farfesa Kperogi Ya Fasa Ƙwai

“Gaskiyar Abin da Ya Jawo Ake Shirin Yin Zanga-Zanga”, Farfesa Kperogi Ya Fasa Ƙwai

  • Shahararren mai sharhi kan lamuran al'umma, Farfesa Farooq Kperogi, ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin yi ranar 1 ga Agusta
  • Farfesa Kperogi ya ce ainihin wadanda suka shirya zanga-zangar, yunwa ce da kuma 'rashin tabbas' da aka shaida a shekara guda da ta gabata
  • A cikin wata wallafa da ya yi, Farfesa Kperogi ya yi tsokaci game da ayyukan 'yan adawa na baya-bayan nan wadanda ya cewa an yarda da su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Atlanta, Amurka - Farfesa Farooq Kperogi, ya ce tushen zanga-zangar da ake shirin yi a Najeriya shi ne hauhawar farashin kayayyakin more rayuwa kamar abinci.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

Farfesa Farooq Kperogi masani ne a harkar yada labarai wanda kuma ke sharhi kan al'amuran al'umma musamman na kasarsa ta gado Najeriya duk da yana zaune a Amurka.

Farfesa Farooq Kperogi ya yi magana kan masu daukar nauyin zanga-zanga
Farfesa Farooq Kperogi ya bayyana goyon bayansa ga masu zanga-zangar ‘kawo karshen mulki mara kyau’. Hoto: Farooq Kperogi
Asali: Facebook

A wata wallafar Farfesa Kperogi ta ranar Asabar, 27 ga watan Yuli, ya tabbatar da cewa 'bacin rai da ya mamaye talakawa shine babban karfi' na zanga-zangar da ake shirin yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Masu daukar nauyin zanga-zanga" - Kperogi

Farfesa Kperogi ya wallafa cewa:

"Mutanen da ke jefa 'yan kasar a cikin mawuyacin hali kuma kullum suna rera masu wakar cewa za su kawo masu canji, ba za su ga da kyau ba idan hakurin talaka ya kare.
"Daga lokacin da jama'a suka farga, ba sa bukatar wani ya jagorance su suyi zanga-zanga. Yunwar cikinsu, cire tsammani kadai za su iya jagorantarsu wajen adawa da 'yan siyasa."

Farfesa Kperogi ya yarda cewa 'yan siyasar adawa na amfani da wannan shirin zanga-zangar domin gurgunta gwamnatin Bola Tinubu, wanda a cewarsa abu ne da ke kan ka'ida.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri: Ministan Tinubu ya ba 'yan Arewa shawari kan zanga-zangar da ake shirin yi

Tinubu ya yi zanga-zanga a mulkin soja

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya yi zanga-zangar lumana kala-kalaa lokacin mulkin soja domin dawo da dimokuradiyya.

Sai dai Shugaba Tinubu ya ce bai taba shiga zanga-zangar da ta tayar da hankalin jama'a ba don haka yake gargadin masu shirin yin zanga-zangar 1 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.