Sarautar Kano: Bidiyon Mazauna Unguwannin Jihar Sun Yi Mubaya'a ga Aminu Ado

Sarautar Kano: Bidiyon Mazauna Unguwannin Jihar Sun Yi Mubaya'a ga Aminu Ado

  • Yayin da ake ci gaba da rigima kan masarautun jihar Kano, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado ya karbi bakwancin alumma a fadarsa
  • Al'ummar wasu unguwanni daga jihar Kano ne suka kai wa Aminu Ado Bayero ziyara domin nuna goyon bayansu gare shi
  • Unguwannin sun hada da Kankarofi da Gwangwazo da Soron Dinki da kuma Kabara inda suka yi mubaya'a tare da addu'o'i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Dandazon al'ummar unguwanni da dama sun kai ziyara fadar sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero a jihar.

Mazauna unguwannin Soron Dinki da Gwangwazo da Kankarofi da kuma Kabara ne suka kai ziyarar fadar Aminu Ado.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

Mazauna unguwannin Kano sun kai ziyara fadar Aminu Ado Bayero
Wasu mazauna unguwannin jihar Kano sun yi mubaya'a ga Aminu Ado Bayero. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Kano: Mazauna unguwanni sun ziyarci Aminu Ado

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da masarautar Kano ta wallafa a shafin X a yau Lahadi 28 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, an gano yadda wakilan unguwar ke shiga fadar Aminu Ado sahu-sahu domin caffan ban girma.

Masu ziyarar sun shiga fadar ne domin nuna goyon baya da mubaya'a da kuma zuba ruwan addu'o'i ga basaraken.

An yi ta shigar da bakin daki-daki kuma a lokuta daban-daban domin gabatar da dalilin zuwansu fadar saboda bin tsarin masarauta.

Musabbbin rigimar masarautu a jihar Kano

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tababa kan masarautar Kano tsakanin Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Rigimar ta fara ne tun bayan tuge Aminu Ado da kuma dawo da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarautar jihar.

Kara karanta wannan

"A rungumi zaman lafiya": Malam Izala da Darika sun yi magana bayan ganawa da Tinubu

Hakan ya biyo bayan rushe masarutun da Gwamna Abba Kabir ya yi wanda tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkira a lokacin mulkinta.

Kano: Aminu Ado ya halarci saukar Alkur'ani

A wani labarin, kun ji cewa sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya samu halartar saukar karatun Alkur'ani mai girma a jihar.

An gayyaci Aminu Ado saukar karatun a masallacin marigayi Isyaka Rabiu inda dandazon jama'a suka tarbe shi cikin farin ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.