Sheikh Abdulaziz Dutsen Tanshi Ya Fadawa Tinubu Mataki 1 da Zai Cire Talaka Daga Wahala

Sheikh Abdulaziz Dutsen Tanshi Ya Fadawa Tinubu Mataki 1 da Zai Cire Talaka Daga Wahala

  • Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya yi kira ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta maido tsarin tallafin man fetur
  • Malamin musuluncin ya ce idan zancen gaskiya ake so, ya zama dole gwamnati ta karya farashin fetur a Najeriya
  • Bayan nan kuma ya soki tsarin da CBN ya bi na sakin farashin Naira a kasuwa, ya ce an dauko fadan da babu riba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya tofa albarkacin bakinsa a lokacin da mutane su ke kokawa da kuncin rayuwa a Najeriya.

A yayin da wasu ke cewa ayi zanga-zanga, babban malamin ya nuna dole a dauki matakai idan ana so talaka ya samu jin dadi da walwala.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi jawabi inda ya dawo da tallafin mai, wutar lantarki? gaskiya ta fito

Bola Tinubu
Sheikh Idris Dutsen-Tanshi ya ba Bola Tinubu shawarar maido tallafin fetur Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

A maido tallafin fetur - Sheikh Idris Dutsen-Tanshi

A wani bidiyo da Zakariyyah El-Uthman ya daura a X, an ji Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya kawo shawarar maido tallafin fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin yake cewa tun farko shugaba Bola Tinubu bai tuntubi jama’a ba, bai yi shawara da majalisa ba sai ya yi watsi da tsarin tallafin.

Saboda haka Idris Dutsen Tanshi ya ce Tinubu ya sanar da maido biyan tallafin fetur.

Hayaniyar zanga-zanga ko tallafin fetur

"Dama ba ‘yan majalisa ne suka yi kudiri aka kawo doka ba. Kai kadai ka yi a matsayinka na Tinubu."
"Yanzu ma kai kadai sai ka yi (dawo da tallafin man fetur), ba shikenan ba?"
"Amma fa idan ka na so a zauna lafiya, komai ya tafi daidai. Shikenan. Idan ba haka ba, wannan hayaniya ba za ta kare ba, yanzu ma aka fara."

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

- Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi

Shehin malamin ya ce gaskiyar magana dole a maido tallafin fetur da aka cire a 2023 domin mutanen kasar nan su samu saukin rayuwa.

Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi kan Naira

A bangaren karya Naira da bankin CBN ya yi, Dutsen Tanshi ya na ganin sai an komawa tsarin da aka sani lokacin gwamnatin baya.

"Maganar Naira ta samawa kanta farashi, ba ta isa ba. An ba Naira fadan da ya fi karfinta."

- Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi

A ra’ayin malamin, Naira ba zai iya gogayya da irinsu Dalar Amurka ba, dole gwamnati ta tallafawa kudin Najeriyan domin kaya su sauko.

Malamai da Bola Tinubu a Aso Rock

Ana da labari cewa kusan Sheikh Kabiru Gombe bai taba ganin an rutsa shugaba ana fada masa gaskiya kamar Bola Tinubu kwanan nan.

Shugaban kasa ya rufe kofa da Kungiyoyin Izala, Ansarud Deen, Tijjaniya da Qadriyyah a Aso Rock yayin da ake neman yi masa zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng