Abin da Ya Faru da Aka Shiga Taro Daga Tinubu Sai Malamai Inji Sheikh Kabiru Gombe

Abin da Ya Faru da Aka Shiga Taro Daga Tinubu Sai Malamai Inji Sheikh Kabiru Gombe

  • Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da wasu malamai sun ziyarci Bola Ahmed Tinubu
  • Sheikh Kabiru Gombe ya ce sun nusar da shugaban kasa halin tsaro da tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya
  • Malaman musuluncin sun cire tsoro sun fadawa shugaban Najeriya halin al’ummarsa a cewar Kabiru Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya yi karin bayani a game da ziyarar da malamai su ka kai zuwa fadar shugaban Najeriya kwanan nan.

Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya ce malaman musuluncin sun fadawa Mai girma Bola Ahmed Tinubu halin da ake ciki.

Tinubu
Sheikh Kabiru Gombe ya ce malamai sun fadawa Bola Tinubu gaskiya a Aso Rock Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Kamar yadda aka ji bayaninsa a shafin wani Ayuba Rabiu Abdulqadir a Facebook, sakataren Izala ya ce an ankarar da shugaban kasa.

A cewar malamin, tattaunawar tayi zafi har wanda yake wajen taron zai dauka shugaban Izala zai bugi Mai girma Bola Tinubu ne.

Kara karanta wannan

Mai neman takaran shugaban kasa ya dora alhakin zanga zanga a kan Bola Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamai sun yi kira ga Bola Tinubu

Bayan Sheikh Abdullahi Bala Lau ya tofa albarkacin bakinsa, Kabiru Gombe ya ce irinsu Farfesa Salisu Shehu sun yi magana a taron.

"Ban taba ganin shugaba ana fada masa maganar gaskiya ba tare da duba abin da yake so ba kamar jiya"
"Sheikh Abdulrahman Ahmad na Ansarud Deen ya gama yarbanci, ya rika turanci yana fadin duk sakon da ya kamata ya zazzago."
"Farfesa Salisu Shehu ya karba…haka malaman nan, duk abin da ka sani na matsalar ‘dan Najeriya, babu wanda ba su fada masa ba."

- Sheikh Kabiru Gombe

Malamai sun yi awa 3 da Tinubu

Kabiru Gombe ya ce ziyarar da aka yi tunani ba za ta wuce mintuna 30 ba, ta ci awanni uku kuma shugaba Tinubu ya saurari kowa.

Tinubu ya ce saboda zuwan malaman ya tanadi ministoci su halarci zaman domin su ji, kuma su yi bayanin matakan da za a dauka.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, Malaman Izala da Ɗariƙa sun faɗi matsaya kan zanga zanga

A zaman, masu ta-cewa a kan tattalin arziki sun bayyana kokarin da gwamnati ta ke yi kan kuncin rayuwar da al’umma su ke ciki.

Abin da malamai suka fadawa Tinubu

Bayanai sun ce malaman sun yi wa shugaban kasa nasiha ne a fadar Aso Rock a gaban mataimakinsa watau Kashim Shettima.

Sauran mahalarta taron sun hada da Mai ba da shawara a kan tsaro, Nuhu Ribadu da kuma sauran ministocin gwamnatin tarayya.

Su wanene Tinubu ya zauna da su

An ji labari Kungiyoyin Tijjaniya da Qadriyyah a karkashin jagorancin Ibrahim Dahiru Bauchi da Qaribullahi Kabra sun je ziyarci Aso Rock.

An san cewa malamai sun yi tasiri a lokacin da aka samu sabani tsakanin kungiyar ECOWAS da gwamnatin Sojoji da ta karbi mulki a Nijar.

Abdullahi Bala Lau ya yi bayanin rawar ganin da malaman suka taka wannan karo domin a fadawa gwamnatin Bola Tinubu gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng