Abubuwa 7 da Suka Jawowa Gwamnatin Tinubu Zanga Zanga Shekara 1 da Hawa Mulki
Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gamu da fushin mutane musamman matasa saboda tsadar rayuwa da matsin lamba.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abubuwa da-dama su ka taru su ka jawo matasa su ka kudiri niyyar shiga zanga-zanga. Legit ta kawo maku wasu daga cikin dalilan.
Abubuwan da suka jawo zanga-zanga:
1. Farashin man fetur
Tsadar man fetur a sanadiyyar janye tallafi ya taimaka wajen tunzura matasa su shiga yajin aikin 1 zuwa 10 ga watan Agusta 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da janye tallafin da aka yi, abin da yake kara fusata ‘yan Najeriya shi ne har yanzu ana fama da layi a gidajen mai a garuruwa.
2. Tsadar dala da karyewar Naira
Ana kuka da mulkin Bola Tinubu saboda yadda farashin Dala ya tashi a sakamakon karya kudin kasar da bankin CBN ya yi tun a bara.
Tsadar dalar ya jawo farashin kayan da ake saye a ketare su ka tashi. Duk da alkawuran da ake yi, har yanzu $1 ta fi karfin N1, 500.
3. Facaka da dukiyar al’umma
Ana zargin gwamnatin tarayya da facaka da dukiyar al’umma a lokacin da ake kukan talaka ya kara hakuri da halin da ya samu kan shi.
Gwamnatin APC mai-ci ta batar da biliyoyin kudi wajen sayen motoci ban da yunkurin nemawa fadar shugaban kasa sabon jirgin sama.
4. Tsare-tsaren gwamnatin Tinubu
BBC ta ce an dauki matakai domin ganin an rage radadin da ake ciki, wasu daga cikin dabarun sun hada da rabon kayan abinci a jihohi.
Sai dai mutane da yawa sun soki wannan kokari, su na ganin tallafin bai kai ga inda ake bukata kuma ba zai iya magance matsalar yunwa ba.
5. Tsada da tashin farashin kaya
Ganin yadda kaya musamman abinci su ka tashi a kasuwa ya harzuka mutane. Aljazeera ta ce ana ganin akwai laifin manufofin Bola Tinubu.
Magidanta sun ce mana ba su iya yin cefane a halin da ake ciki. Ana bukatar akalla N3000 a kullum yayin da hanyoyin samu suka tsuke a yau.
6. Zargin rashin gaskiya
Akwai jami’an gwamnati da ake tuhuma da rashin gaskiya amma ba a ji irinsu hukumomin EFCC, ICPC, NFIU da sauransu sun yi nasara a kansu ba.
Legit ta lura shirin da aka ji game da wadanda ake bincike bai yi wa jama’a dadi sannan ana zargin EFCC ta buge da kama masu kananan laifi.
7. Jinkirin karin albashi
Daidai lokacin da rayuwa tayi kunci, an yi tunanin gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Bola Tinubu za ta kara albashin ma’aikata.
An shafe watanni ba a kai ga karin albashin ba duk da an amince da karin N70, 000 a majalisa. A baya an yi ta kokarin biyan ma’aikata N35, 000.
Yunkurin hana zanga-zanga
Yayin da aka hango hadarin zanga-zanga, rahoto ya zo cewa a gurguje gwamnati ta amince da kudirin mafi karancin albashi da wasu matakai.
Wasu suna alakanta daukar aikin da ake shirin yi a NNPC da ba kananun hukumomi 'yancin kai duk a yunkurin hana matasa zanga-zanga.
Asali: Legit.ng