Ifeanyi Ubah: Muhimman Abubuwan Sani Dangane da Sanatan APC da Ya Rasu

Ifeanyi Ubah: Muhimman Abubuwan Sani Dangane da Sanatan APC da Ya Rasu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Sanatan da ke wakiltar Anambra ta Kudi a majalisar dattawa, Sanata Ifeanyi Ubah, ya riga mu gidan gaskiya.

Kakakin Majalisar Dattawa, Yemi Adaramodu, ya tabbatar da mutuwar Ifeanyi Ubah a ranar Asabar, amma bai bayar da cikakken bayanai ba.

Sanata Ifeanyi Ubah ya rasu
Sanata Ifeanyi Ubah ya rasu yana da shekara 52 a duniya Hoto: Senator Ifeanyi Ubah
Asali: Twitter

Sanata Ubah wanda har zuwa rasuwarsa ɗan jam'iyyar APC ne, ya rasu yana da shekara 52 a duniya, da yana raye da ya cika shekara 53 a ranar 3 ga watan Satumban 2024.

Abubuwan sani dangane da Ifeanyi Ubah

Ga muhimman bayanai guda biyar game da ɗan siyasan kuma hamshaƙin ɗan kasuwa waɗanda jaridar Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Sunayen Sanatoci da ‘Yan majalisar tarayya 6 da mutuwa ta dauke bayan cin zaben 2023

Tasowa da karatun Ifeanyi Ubah

An haifi Ifeanyi Ubah a ranar 3 ga watan Satumba, 1971. Shi ne ɗan farko cikin ƴaƴa bakwai da Mista da Misis Alphonsus Ubah suka haifa a Otolo, da ke Nnewi a jihar Anambra, cewar rahoton jaridar The Punch.

Sakamakon gazawar iyayensa wajen ɗaukar nauyin karatun ƴaƴansu da ɗawainiyarsu, Ifeanyi Ubah ya bar makarantar Premiere academy, Lugbe, Abuja domin koyon kasuwanci tun yana ƙarami.

Kasuwanci

Sanata Ifeanyi Ubah ya zama mai fitar da tayoyin mota da kayayyakin gyara musamman a ƙasashen Yammacin Afirka da suka haɗa da Ghana da Sierra Leone da Liberia.

Daga baya ya faɗaɗa harkokin kasuwancinsa zuwa ƙasashen Turai da suka haɗa da Belgium da Ingila.

A shekarar 2001, ya kafa kamfanin Capital Oil and Gas Limited. Shi ne wanda ya kafa jaridar The Authority Newspaper.

Marigayin shi ne mamallakin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ifeanyi Ubah F.C., wacce ke taka leda a gasar firimiya ta Najeriya, bayan siyan ta a matsayin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Gabros International.

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Majalisar Dattawa ta sanar da mutuwar fitaccen sanatan APC

Siyasa

A shekarar 2014, Ifeanyi Ubah ya sha kaye a zaɓen gwamnan jihar Anambra a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party.

A ranar 24 ga watan Fabrairun 2019, an ayyana Ifeanyi Ubah a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Anambra ta Kudu a ƙarƙashin jam'iyyar YPP, amma ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Ya sake lashe zaɓen sanata a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar YPP a zaɓen 2023, inda daga bisani ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Iyalan Ifeanyi Ubah

Ifeanyi Ubah yana auren Uchenna Ubah, wacce ta yi digiri a fannin harkokin kasuwanci a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, suna da ƴaƴa guda biyar.

Yunƙurin kashe Ifeanyi Ubah

A watan Satumban 2022, ƴan bindiga sun farmaki Sanata Ifeanyi Ubah a Enugwu-Ukwu a kan hanyarsa ta zuwa Nnewi a jihar Anambra.

Ƴan bindigan sun buɗewa ayarin motocinsa wuta inda suka kashe aƙalla mutane biyar da suka haɗa da ƴan sanda biyu.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan Sanatan APC mai ci ya riga mu gidan gaskiya

Ifeanyi Ubah ya tsira da ransa saboda motar da yake ciki harsashi ba ya ratsa ta.

Majalisa ta tabbatar da rasuwar Ifeanyi Ubah

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da mutuwar sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah.

Mai magana da yawun majalisar, Yemi Adaramodu, shi ne ya tabbatar da rasuwar Sanata Ubah ranar Asabar, 27 ga watan Yuli, 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng