Kano: Maganganu 3 da Sanusi II Ya Yi Bayan Ya Dawo Sarauta da Suka Yamutsa Hazo

Kano: Maganganu 3 da Sanusi II Ya Yi Bayan Ya Dawo Sarauta da Suka Yamutsa Hazo

  • Tun bayan dawowar sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan karaga, ya yi maganganu a wurare mabanbanta a cikin Kano
  • Daga cikin maganganun da sarkin ya yi, wasu sun tayar da kura inda jama'a suka masa martani mai zafi daga fadin Najeriya
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku maganganu uku da Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi da suka tayar da kura

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tun bayan da Abba Kabir Yusuf ya dawo da mai martaba Muhammadu Sanusi II kan karaga, sarkin ya yi maganganu iri-iri.

Wasu daga cikin maganganun sun jawo masa suka daga al'ummar Najeriya ganin bai kamata ya yi su ba.

Kara karanta wannan

Ba a gama rikicin sarauta ba, Sanusi II ya ba masu unguwa umurni

Sanisi II
Sanusi II ya yi maganganu da suka jawo cece ku ce a Najeriya. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku jerin kalaman sarkin guda uku da suka kawo masa suka a fadin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II ya yi huduba kan imani ƙaddara

A yayin da ya fara gabatar da huɗubar sallar Juma'a, Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan muhimmancin yarda da kaddara.

Sai dai mutane sun masa rubdugu kan cewa shi ma da ya yarda da kaddara da bai dawo kan mulki ba.

Legit ta ruwaito cewa sarkin ya sha suka ne musamman wajen masu kallon huɗubar kira ne ga mai martaba Aminu Ado Bayero a kan ya rungumi ƙaddara kan tsige shi da aka yi.

Sanusi II ya koka kan wahalar rayuwa

A lokacin da gwamnan Kano ya kaddamar da sayar da takin zamani, Sanusi II ya nuna damuwa kan yadda al'ummar Najeriya ke shan wahala.

Kara karanta wannan

Tinubu: Fitaccen Sarki ya aika muhimmin saƙo ga matasa masu shirin yin zanga zanga

Maganar da ya yi ta jawo masa suka sosai musamman lura da yana cikin masu ba gwamnati shawara kan cire tallafin mai wanda hakan ne ya jefa al'umma a wahala.

Magana kan sarautar Aminu Ado a Kano

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sanusi II ya ce Aminu Ado Bayero ya nuna takaici kan sauke shi ne saboda zai rasa alfarmar da masu mulki ke samu.

Wannan magana ma ta jawo ce-ce-ku-ce yadda mutane suka masa martani kan cewa ai shi ma abin da ya dawo da shi kenan.

Sanusi II ya yi kira kan dasa bishiya

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ba masu rike da sarauta a jihar su ba da gudunmawa wajen shirin shuka bishiyoyi a jihar.

Muhammadu Sanusi II ya yi bayanin ne yayin bikin kaddamar da shuka bishiyoyi na shekarar 2024 da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng