'Yan Majalisa Daga Arewa Sun Ba Mutanen Yankinsu Muhimmiyar Shawara Kan Zanga Zanga
- Ƴan majalisar wakilai da suka fito daga yankin Arewa masu Yamma sun buƙaci mutanen yankin da kada su fito zanga-zanga
- Ƴan majalisar sun bayyana cewa ya sha fama da hare-hare a baya waɗanda suka lalata ababen more rayuwa saboda haka yanzu ba lokacin zanga-zanga ba ne
- Sun buƙaci mutane da su ƙara ba gwamnati dama domin shawo kan matsalolin da ke ta ƙorafi a kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƴan majalisar wakilai daga yankin Arewa maso Yamma sun tofa albarkacin bakinsu kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Ƴan majalisar sun buƙaci al’ummar yankin da kada su shiga zanga-zangar wacce aka shirya fara gudanarwa a ranar, 1 ga watan Agustan 2024.
Shugaban ƙungiyar ƴan majalisar da suka fito daga yankin, Sada Soli, ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sada Soli ya bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma ya sha fama da munanan hare-hare, waɗanda suka lalata ababen more rayuwa a yankin.
Wane kira suka yi ga mutanen yankin?
Ya yi kira ga mutanen yankin da su ba gwamnati lokaci domin magance matsalolin da ke addabarsu, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Sada Soli ya bayyana cewa ƴan majalisar da sauran masu ruwa da tsaki a yankin da suka haɗa da shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya da malaman addini ba sa goyon bayan zanga-zangar.
Ya bayyana zanga-zangar a matsayin wacce wasu ɓata gari suka shirya domin mayar da hannun agogo baya a ƙasar nan.
"Muna kira ga mutanen yankin Arewa maso Yamma masu son zaman lafiya da bin doka da oda, waɗanda suka sha fama da taɓarɓarewar zaman lafiyarsu da kada su shiga cikin wannan zanga-zanga da za ta iya haifar da ɓarna."
"A maimakon haka su ba gwamnatoci a matakin tarayya da na jihohi ƙarin dama domin shawo kan matsalolin da ake kuka da su."
- Sada Soli
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Yan majalisa sun ba Tinubu mafita kan zanga zangar da ake shirin yi
- Matakan gaggawa 10 da gwamnatin Tinubu ta dauka daga jin za a shirya zanga zanga
- Bola Tinubu ya gano masu ɗaukar nauyin zanga zanga, ya faɗawa matasa gaskiya
Shettima ya ba ƴan Najeriya shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Ƙashim Shettima ya nuna muhimmancin ɗaukar matakan da suka dace maimakon fitowa kan tituna domin nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng