Korarrun Ciyamomi Sun Yiwa Gwamna Barazanar Dawowa Ofisoshinsu, Sun Ja Daga
- Tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi sun yi barazana ga Gwamna Siminalayi Fubara kan kin bin umarnin Kotun Koli
- Korarrun ciyamomin sun ce idan har bai bi umarnin kotun ba za su dawo bakin aikinsu kamar yadda doka ta tanadar
- Hakan ya biyo bayan sallamarsu da Fubara ya yi tare da nada shugabannin riko a ƙananan hukumomi 23 da ke jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Tsofaffin shugabannin kananan hukumomi a jihar Rivers sun yi barazanar dawowa ofisoshinsu.
Korarrun ciyamomin sun bayyana haka ne bayan hukuncin Kotun Koli kan ƴancin ƙananan hukumomi a Najeriya.
Rivers: Tsofaffin ciyamomi sun yi barazana
Tsofaffin ciyamomin da ke biyayya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike sun bayyana haka ne a yau Juma'a 26 ga watan Yulin 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suka ce idan har Gwamna Siminalayi Fubara bai bi umarnin kotun ba to tabbas za su dawo bakin aikinsu.
Tsohon shugaban karamar hukumar Emohua, Dakta Chidi Lloyd ya ce sun yi ta jira ko Fubara zai bi umarnin kotun amma shiru.
Rivers: An yi wa ciyamomi gargadi
Lloyd ya ce gwamnan ya yi kunnen uwar shegu da hukuncin inda ya ke ci gaba da tafiya da shugabannin riko a jihar.
Ya ce hakan zai kawo rigima a jihar inda ya bukaci ƴan sanda su dakatar shugabannin riko daga mukamansu.
Har ila yau, ya gargadi shugabannin riko da su guji zuwa wuraren aiki idan kuma ba haka ba za a yi ta kare kowa ya fahimci dokar Kotun Koli.
Wannan na zuwa ne bayan korar shugabannin kananan hukumomi har guda 23 da ke fadin jihar bayan wa'adinsu ya kare a watan Yunin 2024.
Gwamnan Kebbi ya kori shugabannin kananan hukumomi
Kun ji cewa Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya tabbatar da sallamar shugabannin kananan hukumomi 21 a fadin jihar baki daya.
Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne bayan wa'adin tsofaffin ciyamomin ya kare yi a watan Faburairun 2024 da ta gabata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar zaben jihar (KESIEC) ta shirya gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a watan Agusta 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng