Maganar Dangote Ta Fara Fitowa, Najeriya Ta Kashe $2.2bn a Shigo da Mai Daga Malta

Maganar Dangote Ta Fara Fitowa, Najeriya Ta Kashe $2.2bn a Shigo da Mai Daga Malta

  • Alhaji Aliko Dangote ya fara fitowa ya zargi manyan NNPCL da mallakar matatun danyen mai a can nahiyar Turai
  • Mai kudin na Afrika ya ce akwai ‘yan kasuwan da suka bude matatu a yankin kasar Malta, ana tace mai a wajen
  • Bayan Dangote ya yi wannan zargi, sai aka tabbatar da cewa man da ake shigo da shi daga Malta ya karu sosai

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kwanaki kadan bayan babatun Alhaji Aliko Dangote, wasu bayanai sun fara fitowa wadanda za su iya tabbatar da gaskiyarsa.

A sakamakon sabaninsa da gwamnatin tarayya, attajirin ya yi zargin cewa wasu jami’an NNPCL sun mallaki matatun mai a kasar Malta.

Maganar Dangote
Aliko Dangote ya zargi wasu manya da mallakar matatu a kasar Malta Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton da aka samu daga Stati Sense a X ya tabbatar da cewa man da ake shigo da shi Najeriya daga Malta ya karu sosai a 2023.

Kara karanta wannan

Matakan gaggawa 10 da gwamnatin Tinubu ta dauka daga jin za a shirya zanga zanga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels ta ce alamu na nuna Najeriya mara manyan matatun da ke aiki ta shigo da man da ya kai $2.25bn daga kasar Turan a shekara tara.

Man da aka shigo da shi daga Malta

A shekarar 2013, abin da aka kashe domin shigo da mai daga Malta bai wuce $47.3m ba, a 2023 kuwa rahotanni sun ce an kashe $2.8bn.

Punch a rahoton da ta fitar ta ce $59.98m, $117.01m da $13.32m aka kashe wajen shigo da mai daga kasar Turan a 2014, 2015 da kuma 2016.

Tsakanin 2017 zuwa 2022, Najeriya ba ta shigo da wani mai da aka tace a Malta ba. Kwatsam sai aka ga labarin ya canza a shekarar 2023.

Malta: Asalin abin da Dangote ya fada

"Wasu daga cikin ma’aikatan NNPC da wasu ‘yan kasuwa sun bude wurin tace mai a wani wuri a Malta. Mun san wadannan wuraren. Mun san abin da suke yi."

Kara karanta wannan

Bayan kamfanin NNPCL ya bayyana shirin daukar aiki, shafinsa ya tsaya cak

- Aliko Dangote

Wannan lamari ya jawo wasu su ka fara zargin cewa akwai kanshin gaskiya a kan batun Dangote da ya ce akwai masu matatu a Malta.

The Cable ta ce kamfanin NNPCL ne kadai yake shigo da mai yanzu kuma ana kashe $25bn domin kawo mai daga kasashen waje a shekara.

Karin bayani game da kasar Malta

Malta wata Jamhuriyya ce da ke a Kudancin nahiyar Turai da babban birninta yake Valleta kuma wasu akwai kamfanonin mai kasar.

Legit Hausa ta fahimci adadin mutanen kasar a 2022 sun haura 530, 000 kuma mutanen garin su na amfani da harshen Maltese da Ingilishi.

Kwankwaso ya ba Dangote kariya

Kwanan nan rahoto ya zo cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tsoma baki kan rigimar da ake yi game da matatar nan ta Aliko Dangote.

Kwankwaso ya ce ya ziyarci matatar inda ya sha mamaki kan irin ingancinta, ya shawarci gwamnatin Bola Tinubu ta guji tada wata kura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng