Bayan Kamfanin NNPCL ya Bayyana Shirin Daukar Aiki, Shafinsa ya Tsaya Cak
- Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bayyana cewa ya bude kofar daukar ma'aikata da za su taimaka wajen cigaban ayyukan shi
- Awanni da wallafa shafin da jama'a za su shiga domin nuna sha'awar a dauke su aiki a kamfanin ne kuma aka gano ba ya yi
- Kamfanin ya dawo ya yi karin bayanin cewa jama'a ne su ka yiwa shafin yawa, shi ya sa aka fuskanci matsala amma za a dauki mataki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya bayyana cewa ya yi shirin fara daukar ma'aikata a matakai daban-daban domin aiki a kamfanin.
Sai dai bayan wallafa wannan sanarwa a shafukan sada zumuntar NNPCL ne aka gano cewa shafin da aka bayar ba ya aiki.
Kamfanin NNPCL ya wallafa a shafinsa na X cewa zai ci gaba da karbar bukatar daukar aiki daga 'yan Najeriya har 20 Agusta, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL: Shafin daukar aiki ba ya yi
Bayan wallafa tallar daukar mutane aiki a kamfanin NNPCL, 'yan Najeriya da su ka shiga shafin sun gano ba ya aiki.
Wasu da su ka wallafa sakonnin su a shafin Facebook na kamfanin sun zarge su da kokarin fito da shirin da zai kawar da hankalin 'yan kasa daga zanga-zanga.
Collins A Atoberuru ya ce ;
" Mutane sun yi magana da murya daya, ban taba ganin inda NNPC ta bayyana shirin daukar aiki ga jama'a ba, amma yanzu tsoron zanga-zangar gama gari."
NNPCL ya fadi dalilin tsayawar shafinsa
Kamfanin NNPCL ya bayyana dalilin da ya sa aka samu matsala da shafinsa da ya wallafa na daukar jama'a aiki.
A sakon da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa cunkosun mutane ne ya tsayar da shafin, amma ta kokarin gyara.
Kamfanin NNPCL ya fadi dalilin tsadar mai
A baya kun ji cewa shugaban kamfanin man fetur na kasa ( NNPCL) ya bayyana dalilin da ya sa ake samun dogayen layin fetur a gidajen mai da ke fadin kasar nan.
Kamfanin ya dora alhakin hakan a kan mamakon ruwan sama da aka samu, inda ya kara da cewa ya kawo tsaiko wajen safarar fetur zuwa gidajen mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng