“A Rungumi Zaman Lafiya”: Malam Izala da Darika Sun Yi Magana Bayan Ganawa da Tinubu

“A Rungumi Zaman Lafiya”: Malam Izala da Darika Sun Yi Magana Bayan Ganawa da Tinubu

  • Malaman addininin Musulunci sun ce za su ci gaba da taya gwamnati da addu'a da kuma kara kaimi wajen fadakar da al'ummar kasar
  • Hakazalika, malaman kungiyoyin Darika da Izala sun jaddada cewa zaman lafiya shi ne abin da Najeriya ta fi bukata a halin yanzu
  • Wannan na zuwa ne bayan malaman sun gana da Shugaba Bola Tinubu a Abuja inda suka tattauna kan tattali da kuma zanga-zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Malaman addinin Musulunci da suka hada da na bangaren Izala da Darika sun gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

An ce wannan tattaunawar ta mayar da hankali ne kan tattalin arziki, sha'anin mulki da kuma batun zanga-zangar da ake shirin yi a ranar 1 ga Agusta.

Kara karanta wannan

A kara hakuri, tattalin arziki na dab da gyaruwa: Abin da Tinubu ya fadawa sarakuna

Malaman addinin Musulunci sun yi magana kan zaman lafiya a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya gana da malaman addinin Musulunci a Abuja. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Kamar yadda fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na X, malam addinin sun samu jagorancin Sheikh Bala Lau, wanda kuma shi ne shugaban Izala na kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamai za su taya Tinubu da addu'a

A nasa jawabin, jagoran tawagar malaman addinin, Sheikh Bala Lau ya baiwa shugaban kasar tabbacin bada goyon baya, addu'o'i da karin fadakarwa ga 'yan Najeriya.

“Zaman lafiya shi ne babban abu a gare mu a kasar nan. Abu na farko da Ibrahim AS ya roki Allah shi ne zaman lafiya da shiriya.
"Za mu ci gaba da gwamnati goyon baya tare da taya ta da addu'a, yayin da kuma za mu kara kaimi wajen fadakar da al'umma."

- In ji Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Bola Tinubu ya yi magana kan zanga-zanga

Shugaban kasa Bola Tinubu ya shaidawa tawagar malaman cewa masu daukar nauyin gudanar da zanga-zangar sun dora burinsu na son rai fiye da kishin kasa.

Kara karanta wannan

"Ban da lalata kadarori": Tinubu ya fadi yadda ya shiga zanga zanga a lokacin soja

Tinubu ya kara da cewa:

“Masu daukar nauyin zanga-zangar ba sa kaunar kasarmu. Ba su da soyayya ga al'umma. Ba su fahimci muhimmancin zama ɗan ƙasa ba, watakila suna da fasfo na barin kasar ne."
"Ba za mu so Najeriya ta koma kamar Sudan ba. Muna maganar yunwa ne ba binne gawarwaki ba. Ya kamata mu yi taka tsantsan da siyasar tsana da fushin wani."

Babu 'yan bani na iya a gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bola Tinubu ya ce babu 'yan bani na iya da suka yi kaka gida a gwamnatinsa da har ake tunanin su ke yin zagon kasa ga tattalin arziki.

Shugaban kasar ya jaddada cewa shi ne ya dauki nauyin yakin neman zabensa don haka babu wanda ke binsa bashi da zai iya juya akalar gwamnatinsa a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.