Tsadar Rayuwa: DSS Ta Gano Inda Matsalar Take, an Cafke Barayin Abincin Tallafi a Arewa
- Rahotanni sun bayyana cewa jami'an DSS sun cafke wasu bata gari a jihar Katsina da suka sace buhuna 2,000 na shinkafar tallafi
- A makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta rabawa jihohi tirela 740 na shinkafa domin su rabawa talakawansu na rage talauci
- Sai dai an gano cewa kason Katsina na isa jihar, wasu suka yi sama da fadi da buhuna 2,000 tare da rarrabawa shaguna su sayar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Hukumar DSS ta ce jami'anta sun cafke wasu da ake zargin sun karkatar da daruruwan buhunan shinkafa da gwamnatin tarayya ta aika zuwa Katsina.
A makon da ya gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya amince a raba tirela 740 na shinkafa ga jihohi 36 da Abuja domin a rabawa talakawa da niyyar rage raɗaɗin talauci.
An cafke barayin abincin tallafi
Sai dai rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa an samu wasu bata gari da suka yi sama da fadi da daruruwan buhunan shinkafar da aka tura Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce an cafke barayin shinkafar ne a ranar Laraba a babbar kasuwar Katsina yayin da suke saukewa shaguna shinkafar da nufin sayarwa.
Rahoton ya ce an kama sama da buhuna 2,000 na shinkafar satar a shaguna daban daban inda aka boye su domin sayarwa a sirrance.
Ana zargin sa hannun jami'an gwamnati
An kuma ce wadanda aka kama sun bayar da wasu muhimman bayanai da za su taimaka wajen cafke wadanda ke da hannu a karkatar da abincin.
Akwai wasu jami'an gwamnatin jihar Katsina da aka ce akwai hannunsu a cikin satar, sai dai ba a iya tabbata da wannan ikirarin ba, inji jaridar The Guardian.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na jihar Katsina, Alhaji Shehu Usman, ya ce wani wanda ba dan kasuwar ne ba ya shigo da shinkafar aka rabawa shaguna.
Gwamnan Katsina zai raba abincin tallafi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Raɗda ya shirya ciyar da mutane 2,166,000 masu ƙaramin karfi a tsawon kwanakin watan Ramadan.
Malam Dikko Umaru Raɗɗa ne ya bayyana haka a wurin kaddamar da kwamitin da zai jagoranci raba tallafin a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng