Harkar Noma: Gwamnatin Kano ta Ware Biliyoyi Domin Aikin Madatsar Ruwa

Harkar Noma: Gwamnatin Kano ta Ware Biliyoyi Domin Aikin Madatsar Ruwa

  • Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudurin karfafa noman rani da damuna domin bunkasa samar da abinci
  • Wannan ya sa gwamnati ta amince da fitar da Naira biliyan 2.5 domin aikin madatsar ruwan Kafin ciri
  • Aikin hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jiha, bankin raya musulunci da kuma asusun the lives and livelihoods

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta amince da fitar da Naira Biliyan 2.5 domin aikin madatsar ruwa Kafin ciri a karamar hukumar Garko.

Aikin zai zo ne ta karkashin shirin gwamnati na habaka noma da kiwo (KSADP) wanda ya ke samun tallafi daga bankin raya musulunci da gidauniyar the lives and livelihoods.

Kara karanta wannan

Gwamnoni da wasu ministoci sun fara koƙarin hana matasa zanga zangar da suke shirin yi

Jihar Kano
Gwamnati ta ware N2.5bn domin aikin madatsar ruwan Kafin ciri Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugaban shirin na Kano, Ibrahim Garba Muhammad ya ce makasudin shirin shi ne habaka bangaren noma da samawa matasa aikin yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Noman rani: Gwamnati za ta fadada gonaki

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta fadada gonar noman rani da damuna zuwa kadada 419 a karamar hukumar Garko domin habaka samar da abinci, Solace Base ta wallafa.

Shugaban shirin KSADP, Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana haka, inda ya ce da farko sun yi niyyar samar da karin kadada 1000 a wajen noman ranin Watari.

Dalilin fadada gonar Kafin ciri a Kano

Gwamnatin Kano ta ce an dakatar da aikin gonar Watari saboda gwamnatin tarayya na shigen aikin a wurin, shi yasa aka dawo da aikin a Kafin ciri.

Gwamnatin ta ce za a gudanar da aikin ne ta hanyar daukar kudin aikin Watari bayan samun sahalewar bankin raya musulunci na duniya na sauya wurin aikin.

Kara karanta wannan

Yaki da talauci: Tinubu ya yiwa jihohi 34 yayyafin N438bn ana shirin zanga zanga

Za a raba taki ga manoma

A baya mun kawo labarin cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya aikawa talakawan Kano tirelolin taki domin rabawa ga manoma.

Za a raba tirelolin taki 69 ga manoma a kananan hukumomin jihar domin habaka noma da samar da abinci a dai-dai lokacin da damuna ke ci gaba da kankama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.