“Ban da Lalata Kadarori”: Tinubu Ya Fadi Yadda Ya Shiga Zanga Zanga a Lokacin Soja

“Ban da Lalata Kadarori”: Tinubu Ya Fadi Yadda Ya Shiga Zanga Zanga a Lokacin Soja

  • An yi kira ga 'yan Najeriya da su yi zanga-zangar lumana tare da kaucewa tada husumar da za ta hargitsa kasa, rasa rayuka da kadarori
  • Shugaba Bola Tinubu ya yi wannan nasihar ne a ranar Alhamis yayin da ya bayyana cewa 'yan Najeriya na da 'yancin yin zanga-zanga
  • Shugaban ƙasar wanda ya ce shi ma ya taba shiga zanga-zanga ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci tayar da tarzoma a fadin kasar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya yi zanga-zangar lumana kala-kala amma ba ta tayar da tashin hankali ba.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro ta jero mutanen da ake shirin kai wa hari a lokacin zanga zanga

Wannan bayanin da Shugaba Bola Tinubu ya yi yana da alaƙa da zanga-zangar da ake shirin yi a ranar 1 ga watan Agusta wanda ya janyo damuwa mai yawa.

Bola Tinubu ya yi magana kan masu shirin yin zanga-zanga a Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba da labarin zanga-zangar da ya yi a zamanin soja. Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Tinubu ya ja kunne kan lalata dukiyoyi

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan yayin da ya karɓi wasikar turo sabon jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin cigaban damokaraɗiyya, inda yace zanga-zanga wani babban yanki ne a damokaraɗiyya amma babu gwamnati da za ta lamunci ɓarna.

Shugaba Tinubu ya ce:

"Muna fatan Najeriya da Amurka su cigaba da aiki tare domin yaukaka dankon dangantakar da ke tsakaninmu da kuma cimma manufofi iri ɗaya da tsarukan dimokuradiyya.
”Yayin mulki soja, mun ɗaga muryoyinmu kan mulkin kama-karya, kuma ina daga cikin ƙungiyar da ta yi zanga-zangar lumana ba tare da ɓarnata dukiyoyi ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana jihar Arewa da ba za a yi zanga zanga ba

"Mun yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da ɗorarriyar dimokuradiyya kuma zan cigaba da kiyaye wannan dimokuradiyya."

Dalibai sun janye daga zanga-zanga

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa ƙungiyar ɗaliban Najeriya, NANS, ta bayyana cewa ta janye daga shirin fita zanga-zangar da za yi kan yunwa da matsin rayuwa a Najeriya.

Ƙungiyar ɗaliban da ke makarantu daban daban a jihar Legas ta bayyana cewa za ta yi tattaki ne ba zanga-zanga ba, kuma za ta nuna goyon baya ga gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.