Ba a Gama Rikicin Sarauta Ba, Sanusi II Ya Ba Masu Unguwa Umurni
- A jiya Laraba ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shuka bishiyoyi domin kawo sauyin yanayi a jihar Kano
- Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya kasance babban bako yayin kaddamar da shuka bishiyoyin da gwamnan ya yi
- Muhammad Sanusi II ya ba masu rike da sarautu umurni kan yadda ya kamata su bayar da gudunmawa wajen nasarar shirin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ya yi jawabi na musamman yayin shirin kaddamar da shuka bishiyoyi a Kano.
A yayin taron, Muhammadu Sanusi II ya bayyana muhimmanci da fa'idar da za a samu wajen shuka bishiyoyi a cikin al'umma.
Legit ta tatttaro bayanan da mai martaba sarkin ya yi ne cikin sakon da daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi II ya umurci masu sarauta
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya umurci dukkan masu sarautar gargajiya daga dagatai da masu unguwa su tallafi shirin shuka bishiyoyin.
Muhammadu Sanusi II ya bukace su da su koma yankunan su domin tabbatar da taimakawa aikin shuka itatuwan.
Sanusi II: 'Amfanin shuka bishiya'
Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa hatta a bangaren addini shuka bishiyoyi na da matuƙar muhimmaci saboda haka ya kamata mutane su rungumi aikin.
Bayan haka, ya kara da cewa shuka itatuwa hanya ce da za ta taimaka wajen yaki da dumamar yanayi.
Gwamnan Kano ya mika godiya
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika godiya ga sarkin bisa gudunmawar da yake ba shi wajen kawo cigaba a jihar.
Haka zalika gwamnan ya mika godiya ga al'ummar jihar bisa goyon baya da suke ba shi a kowane lokaci.
Lauya ya yi maganar rikicin sarautar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen lauya mazaunin Kano, Umar Sa'ad Hassan ya bayyana matsayarsa kan kirkirar masarautu uku masu daraja ta biyu.
Lauyan ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan wannan mataki inda ya ce abin a yaba ne kuma zai kawo ci gaba matuka a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng